Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Da Karamar Hukumar Dutse Za Su Shirya Taron Bita Ga Kansiloli
Published: 24th, July 2025 GMT
Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana cewa gudanar da ayyukan raya kasa sosai a yankunan karkara zai kara daga martabar jihar a idon sauran jihohin kasar nan.
Ya yi wannan tsokaci ne yayin ziyarar aiki a sakatariyar karamar hukumar Dutse, inda ya ja hankalin shugaban karamar hukumar game da bukatar bada fifiko ga bangaren ayyukan raya kasa fiye da harkokin yau da kullum domin karfafa matakin cigaban karamar hukumar.
A cewar sa, kwamatin na rangadin kananan hukumomin jihar 27 ne domin bibiyar yadda ake aiwatar da tanade tanaden kasafin kudi domin tabbatar da kashe kudaden gwamnati ta hanyar da ta dace, Inda Kwamatin ke duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin Kudi da nufin cusa dabi’ar aiki da tanade tanaden aikin gwamnatin da ka’idojin kashe kudade.
Kazalika, Alhaji Aminu Zakari yace an kafa kananan kwamitoci guda 2 domin ziyarar gani da ido kan ayyukan raya kasa da karamar hukumar Dutse ta gudanar ga jama’ar yankin.
Karamin Kwamati na daya bisa jagorancin wakilin mazabar
Kanya Babba Alhaji Ibrahim Hashim Kanya, ya duba aikin ginin Masallacin khamsissalawati na garin Barangu da rumfunan kasuwa a garin ‘Yar Gaba da Masallacin khamsissalawati na Gidan Gawo da aikin ginin karamin asibitin garin Charka da aikin karamin asibitin Zangon Buji, da aikin gyaran Masallacin Juma’a na garuruwan Kacha da Barandau.
Shi kuwa karamin kwamati na 2 bisa jagorancin wakilin mazabar Buji, Alhaji Sale Baba Buji ya duba aikin hanyar Burji daga Bolari ta wuce Bakin Jeji zuwa Katangar lafiya, akan naira milyan 129 wadda wani kamfani ya yi, sai kuma rumfar kasuwa a garin Hammayayi da sanya fitilu masu amfani da hasken rana makaranta sikandire ta garin Madobi da Masallacin Juma’a na garin Baranda.
A jawabin sa na maraba, shugaban karamar hukumar Dutse Malam Sibu Abdullahi, ya bayyana ayyukan Kwamatin a matsayin ginshikin samun nasarar gudanar da mulkin kananan hukumomi.
Ya bayyana kudurin sa na karbar gyare-gyare da shawarwarin Kwamatin domin cigaban karamar hukumar sa.
Malam Sibu Abdullahi ya bayyana kudurinsa na hada Kai da majalisar Dokokin jihar Jigawa domin shiryawa kansiloli da Akawun majalisar kamsilolin bita game da tsare tsaren zaman majalisa kamar yadda mataimakin sakataren Kwamatin Malam Sadiq Muhammad ya kawo shawara.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa karamar hukumar Dutse
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.