Gwamnatin Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ana shirin sayar da makarantar firamare ta Yusuf Dantsoho da ke Unguwar Rimi GRA.

 

Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Maman Lagos, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki makarantar.

 

Makarantar Yusuf Dantsoho, wacce aka kafa a shekarar 1920, tana tsakiyar Unguwar Rimi GRA, kuma ta samar da fitattun ‘yan Najeriya da dama da suka yi aiki a matakai daban-daban na gwamnati da kuma masu zaman kansu.

 

Alhaji Maman Lagos ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta da niyyar sayar da wata cibiyar gwamnati, kama daga makarantu zuwa asibitoci.

 

Yace maimakon haka, gwamnati na da kudurin inganta da fadada irin wadannan cibiyoyin domin su fi amfani wa al’umma.

 

Alhaji Maman Lagos ya kalubalanci duk wanda ke da ikirarin ya sayi makarantar da ya fito da takardun shaida.

 

Ya ce gwamnatin Malam Uba Sani ba za ta sayar da makarantu mallakin gwamnati ba.

 

Haka kuma, ya bukaci iyaye da mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu su kuma yi watsi da jita-jita marasa tushe.

 

A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Muhammad Gambo, ya tabbatar da cewa makarantar Yusuf Dantsoho tana karkashin kulawar hukumar kananan hukumomi kamar yadda aka saba.

 

Wani jigo a harkokin makarantar, Abubakar Kantoma, ya bayyana cewa wasu ‘yan gine-gine sun yi yunkurin fara aiki a cikin harabar makarantar, amma aka dakatar da su saboda rashin bayyananniyar hujja.

 

Radio Nigeria ta kuma tattauna da wasu daliban makarantar wadanda suka nuna damuwa kan jita-jitar da ake yadawa.

 

Makarantar dai ta rufe ne a lokacin ziyarar saboda hutun karshen zangon karatu.

COV: Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamnatin Jihar Karyata Makarantar Rade radin Sayarda

এছাড়াও পড়ুন:

Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma’a – Gwamnati

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Ali Haruna Makoda, ya buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci.

Ya yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da ya makara wajen dawowa makaranta zai iya fuskantar hukunci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 3.5 Wajen Gina Shaguna A Farm Centre
  • Wakilin Sin Ya Karyata Amurka Game Da Batun Yankin Xinjiang Na Sin a Taron Kwamitin Sulhun MDD
  • Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato
  • Kwankwaso Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Ware Arewacin Nijeriya A Rabon Arzikin Ƙasa
  • Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu
  • Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza
  • Gwamnatin Bauchi Ta Cire Shugaban Makaranta Kan Satar Kayan Gwamnati
  • Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma’a – Gwamnati
  • Har Yanzu Yaƙi Da Ta’addanci Ne Babban Muradin Gwamnatina — Tinubu