Hukumar Ba Da Agajin Jin Kai Ta ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa Ta “UNRWA” Ta Sanar Da Kashe Ma’aikatan 330 A Gaza
Published: 25th, July 2025 GMT
Hukumar ba da agaji da kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta “UNRWA” tana karkashin wuta sakamakon ma’aikatan 330 da suka yi shahada kuma aka lalata cibiyoyinta 300 a Gaza!
Inas Hamdan, mai magana da yawun hukumar ta UNRWA a birnin Alkahira, ta tabbatar da cewa; Yunwar da ke faruwa a zirin Gaza, wani bala’i ne da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya shafi mutane sama da miliyan biyu, ciki har da akalla yara miliyan daya.
Hamdan ta yi nuni da cewa, a lokacin da suke magana kan matsalar agajin jin kai ko shigar da kayan abinci zuwa zirin Gaza, suna fuskantar shamaki da aka sanya a zirin Gaza, baya ga tsarin rabon da wata gidauniya mai suna Gazan Humanitarian Foundation ke gudanarwa, wanda ke zama tarkon mutuwa. Ya zuwa yanzu, fiye da mutane dubu sun mutu yayin da suke jiran abinci, haƙƙin duk mazauna cikin wannan mawuyacin yanayi.
Ta yi gargadin cewa matakan karancin abinci na ci gaba da tabarbarewa, inda ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba da kuma matukar damuwa. Adadin matsalolin rashin abinci mai gina jiki, musamman a tsakanin yara, yana nuna mummunar tabarbarewa a wannan fanni. Akalla yara 5,500 ‘yan kasa da shekaru biyar ne ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, ciki har da yara akalla 800 da ke cikin matsanancin hali na rashin abinci mai gina jiki, ma’ana suna fuskantar barazanar yunwa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp