Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: Taro Tsakanin Iran Da Tawagar Kasashen Turai Dama Ce Ta Gyarar Tunanin Tarai
Published: 25th, July 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Taron Istanbul wata dama ce ta gyara matsayar Turai kan shirin makamashin nukiliyar Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i, ya yi la’akari da taron na yau tsakanin Iran da kasashe uku mambobin kungiyar hadin gwiwa ta JCPOA a matsayin wata muhimmiyar dama ta gyara ra’ayoyinsu da gwada hakikaninsu kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran.
A cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labaran IRNA, Isma’il Baqa’i ya bayyana fatansa na cewa wadannan kasashe uku za su yi amfani da wannan damar wajen gyara tsarin da suka bi a baya wanda bai dace ba, wanda ya lalata martabar Turai da matsayin tattaunawa, tare da mayar da ita a matsayin yar wasa maras tushe.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana takaicinsa game da matsayin kasashen Turai uku na nuna son zuciya dangane da wuce gona da iri da gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka suka dauka kan kasar Iran – wadanda suka gabatar da wadannan kasashe uku ga duniya a matsayin tushe haifar da hargitsi da mara wa ta’addanci gindi. Ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a baya ta yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da irin wadannan matsayar da ba ta dace ba, kuma tabbas a taron na yau Juma’a za a isar da zanga-zangar Iran dangane da hakan ga bangarorin Turai, kuma za a bukaci su yi karin haske.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun.
Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin Huangyan Dao.
Lin ya ce “Mun gabatar da kakkarfan korafi a yau, dangane da kuskuren da Amurka ta tafka. Tsibirin Huangyan Dao yankin kasar Sin ne tun fil azal”, kuma kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin na karkashin ikon mulkin kai na Sin, wanda hakan ke nufin yana bisa turba, ya dace da doka, bai kuma cancanci suka ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp