Tsibirin Ciniki Maras Shinge Na Hainan Na Ci Gaba Da Jawo Hankalin Jarin Waje
Published: 24th, July 2025 GMT
Aikin gina tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin ya samu gagarumin ci gaba sosai, inda gwamnatin kasar Sin ta sanar a jiya cewa, a ranar 18 ga watan Disamban bana, za a kaddamar da manufar kafa “kwastam mai zaman kansa a duk faɗin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan” a hukumance, wadda ke nufin saukaka bincike da ragewa ko soke haraji.
Ga kasar Sin, gina tsibirin ciniki maras shinge na Hainan wata babbar manufa ce ta kasa, wadda ke nuna matsayin koli na bude kofa ga kasashen duniya.
Bayan aiwatar da manufar, duk tsibirin Hainan zai zama yanki na musamman a karkashin kulawar hukumar kwastam, za a aiwatar da manufofi mafi ’yanci kuma masu sauki, da za su shafi fannoni guda hudu, wato, manufar soke harajin kayayyaki, matakan saukaka harkokin kasuwanci, matakan zirga-zirga masu dacewa da kuma tsarin sa ido mai inganci.
Dauki manufar “soke haraji” a matsayin misali. Bayan manufar ta fara aiki a duk fadin tsibirin Hainan, za a fadada adadin kayayyakin da ba su da haraji daga 1,900 a yanzu zuwa kusan 6,600, wanda ya kai kusan kashi 74 bisa dari na dukkan rukunonin harajin kayayyaki, kuma ya karu da kashi 53 bisa dari idan aka kwatnta da yawan kayayyakin da ake shigowa kafin a aiwatar da manufar. Wannan zai rage dimbin kudaden da ake kashewa wajen shigowa da kayayyaki, da kara kuzarin yin kasuwanci, da kuma samar da riba ga masu sayayya da ’yan kasuwa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, cikakken zama na 4 na kwamiti na 20 na JKS ya amince da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Sin za ta yi amfani da wannan damar don ci gaba da gyare-gyaren tattalin arzikinta, da kuma fadada bude kasuwancinta mai zurfi ga ketare, ta haka za ta ci gaba da ba da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik da sauran kasashen duniya ta hanyar zamanantar da al’ummarta. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA