Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 11 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Sakkwato
Published: 24th, July 2025 GMT
Gobir ya bayyana cewa kowanne daga cikin waɗanda aka ceto zai samu Naira 100,000, buhun gero ɗaya da buhun masara ɗaya a matsayin tallafi.
Shi ma da yake magana, Shugaban ƙaramar hukumar Isa, Alhaji Sherifu Abubakar Kamarawa, ya gode wa gwamnatin jihar bisa taimakon da ta bayar, yana mai cewa hakan ya nuna damuwar gwamnati kan tsaron rayuka da jin daɗin al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Jami an Tsaro Sakkwato Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Sarakuna Sun Bukaci Gwamnati Ta Canza Salo
Kashe- Kashen 2025 Ya Fi Na 2024
Alkaluman bincike sun bayyana cewar ‘yan ta’adda sun dauki rayukan mutane a rabin wannan shekarar fiye da na shekarar 2024 da ta gabata kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yancin Dan- Adam ta kasa ta bayyana a wannan watan.
Kamar yadda alkaluman suka nuna, akalla mutane 2, 266 ne suka bakunci lahira a hannun ‘yan ta’adda a rabin shekarar 2025, idan aka kwatanta da mutane 1, 083 a rabin farko na shekarar 2024 da kuma mutane 2, 194 a bakidaya shekarar.
Rundunar sojojin Nijeriya na fafatawar yaki da mayakan Boko- Haram da sauran ‘yan ta’adda a Arewa Maso- Gabas, ta’addanci da garkuwa da mutane a Arewa Maso- Yamma, hare- haren makiyaya da manoma a Arewa ta- Tsakiya da kuma masu fafatukar neman ‘yanci a Kudu Maso- Gabas.
Lamarin ya yi kamari a kwanan nan a inda aka kashe mutane 606 a watan Yuni da ya gabata kadai ciki har da hare- haren da aka kaiwa al’ummar Yelewata da Dauda a Benue ta tsakiya a inda mutane 200 suka bakunci lahira.
Babban sakataren Hukumar Kula da ‘Yancin Dan- Adam, Tony Ojukwu ne ya bayyana wannan adadin a Abuja tare da kira ga gwamnati da ta dauki kwakkwaran matakin gaggawa domin takawa matsalar burki.
Hukumar ta ce an yi garkuwa da mutane 857 a rabin farko na shekarar 2025, duk da hakan ya ragu a kan mutane 1, 461 da aka yi garkuwa da su a shekarar da ta gabata.
Rahoton ya kuma nuna hare- haren da aka kaiwa hukumomin tabbatar da doka da jami’an tsaro a inda aka kashe sojoji 17 a jihohin Kaduna da Neja da kuma manbobin jami’an tsaron sa- kai na JTF 40 a Zamfara.
Canza Salo Shine Mafita – Sarakuna
A kan yadda yankuna da dama suka zama lahira kusa; sarakunan gargajiya wadanda sune suka fi zama kusa da al’umma sun bukaci canza salon yaki da ‘yan ta’addan ta hanyar daukar kwararan matakan dakile matsalar domin ganin al’umma sun rika bacci da idanu biyu.
Mai Girma Sarkin Bida, Alhaji Yahaya Abubakar ya bayyana cewar lokaci ya yi da ya kamata gwamnati da hukumomin tsaro su canza dubarun kawo karshen matsalar tsaro domin ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo a cikin al’umma.
Ya ce domin samun nasara akwai bukatar masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro su hada kai, ba da gudunmuwa da sake salon tunkarar ayyukan ta’addanci da sauran kalubalen tsaro.
Sarkin Bida wanda shine shugaban majalisar sarakunan jihar Neja ya bayyana cewar matsalar tsaro hakki ne da ya rataya a wuyan dukkanin ‘yan kasa masu bin doka domin shawo kan kalubalen da ke gaban su.
Sarkin wanda ya bayyana hakan a yayin da ya karbi bakuncin sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Neja, Adamu Abdullahi- Elleman a fadarsa a makon jiya ya ce shawo kan matsalar tsaro na bukatar sa hannun sarakunan gargajiya da al’umma bakidaya.
Ya ce a bisa ga yadda ake ci-gaba da fama da matsalar akwai bukatar sake duba sosai, a hada kai, a bada gudunmuwa a kuma sake salon yakar ayyukan ta’addanci.
A yayin da ya ce bai kamata a bar harkokin tsaro da kariyar rayuka da kadarorin al’umma ga hukumomin tsaro da gwamnati kawai ba, ya ce dukkanin al’umma ciki har da shi kan sa ya zama wajibi a gare su, da su taimakawa hukumomin tsaro domin ganin sun samu damar gudanar da aiki yadda ya kamata.
Babban basaraken wanda ke da girma da kima a cikin al’umma ya bayyana cewar hakan ya wajaba domin ganin ‘yan Nijeriya sun rika bacci da idanu daya ba tare da zullumi da fargabar abin da zai iya biyowa baya ba.
A kan wannan sarkin mai daraja ta daya ya bayyana alkawalin ci- gaba da dorewar goyon bayan sarakunan jihar ga rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar domin samun nasarar kawar da ayyukan ta’addanci da dawo da zaman lafiya a cikin al’umma.
Baya ga wannan Sarkin masarautar Iselu, Ebenezer Akinyemi da ke Iselu a jihar Ogun ya bukaci shugaba Tinubu da ya duba yiyuwar dauko hayar sojojin kasar waje domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar nan.
A ta bakinsa ya kamata shugaban kasa ya shirya wata muhawara a majalisar tarayya kan yadda ya kamata a gayyato sojojin kasashen waje a Nijeriya domin su kakkabe ayyukan ta’addanci.
Ya ce daukar wannan matakin zai sa al’ummar kasar nan maza da mata kauracewa goyon bayan masu aikata ta’asar a yayin da aka nemi kashe su a fagen daga.
Ya ce yawaitar zubar da jinin al’umma da ake yi a Nijeriya ya zama abin Allah- wadai a kasar nan wanda wasu ke amfani da kalubalen tsaro a matsayin wata ‘masana’anta.’
Basaraken ya ce idan aka ci-gaba da zama a yadda ake ba tare da daukar kwakkwaran mataki ba to sakamakon da za a samu zai illata hadin kai da kwanciyar hankali a kasa bakidaya.
Ya ce abin takaici ne yadda rayukan al’umma ko kadan ba su da wata daraja a wasu sassan kasa duk da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi wajen kawar da matsalolin tsaro a dukkanin lungu da sakon kasar nan.
Sarkin Iselu ya ce kasar da suka taso suka gani da zaman lafiya a gomman shekaru ta zama wata kasar da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, da fulanin kasar waje ke cin karensu ba babbaka ta hanyar tayar da hankulan jama’a wadanda kuma ba su da wata alamar ajiye makami.
Ya ce ya kamata shugaban kasa ya dauki matakin gaggawa domin haukar kisan gillar al’umma da wasu ke yi ya baiwa wasu damar kafa wata ‘masana’anta’ da suke son a ci-gaba da kashe-karshen har abada.
A kwanan baya ma mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewar Nijeriya na fuskantar tsananin tabarbarewar sha’anin tsaro ta yadda ‘yan ta’adda suka mamaye garuruwa da dama.
Ya ce ‘yan Nijeriya na rayuwa tare da ‘yan ta’adda da mayakan Boko- Haram kamar yadda ya bayyana a taron bukin cika shekaru 60 na tsohon Gwamnan Ribers, Rotimi Ameachi a Abuja a kwanan baya.
Ya ce masu gargadin a kula kafin shiga rikice-rikice, su yi hattara, ya ce jama’a na cikin matsalolin tsaro a yanzu haka don haka abin tambaya shine yaya za a fita daga cikin matsalar?
Gudunmuwar Sarakuna Wajen Samar Da Zaman Lafiya
A bayyane yake cewar sarakuna wadanda suka fi kusanci da al’umma suna da gagarumar gudunmuwar da za su bayar wajen ganin al’ummarsu sun yi bankwana da halin kunci da tashin hankalin da suka jima a ciki na rashin tsaro.
A tsayin lokaci sarakuna sun bukaci canza salon yaki da ta’addanci.
Kusanci da kimar da suke da ita ga al’umma muhimmiya ce wajen wanzar da zaman lafiya don haka ake ganin akwai bukatar gwamnati ta sanya su a cikin aikin samar da tsaro ba wai kawai dogara da hukumomin tsaro ba.
Kasancewar sarakuna na da girma da karbuwa ga al’umma kuma suna hulda da jama’a a kullum don haka suna da tasiri a shiraruwan samar da ingantaccen tsaron da al’umma ke nema.
Haka ma sarakuna wadanda ke da kwarewa wajen kawar da sabanin fahimta da rikice- rikicen zamantakewa na da gudunmuwar bayarwa wajen samun sahihan bayanai a cikin sauki daga mabambantan al’umma.
A kan wannan ne sarakuna a kwanan nan suka sake gabatar da bukatar su ga kwamitin sauraren ra’ayoyin jama’a kan gyaran kundin tsarin mulkin kasa na 1999 kan samar masu gurbi a cikin kundin tsarin mulki wanda hakan zai karfafa masu tare da ba su cikakken ikon sauke nauyin da ke kan su.
A bayyane yake cewar idan har aka yi wa sarakuna tanadi a cikin kundin tsarin mulki to za su samu ikon bayar da gagarumar gudunmuwa ciki kuwa har da hobbasar kwazon kawar da ayyukan ta’addanci da ya jima yana ci masu tuwo a kwarya.
Domin daukar kwararan matakan kawar da matsalar tsaro a yankunan su, sarakunan Arewacin Nijeriya a watannin baya sun gudanar da taron musamman domin yakar matsalolin ayyukan Boko- Haram, ta’addanci da garkuwa da mutane.
Taron wanda aka gudanar a Maiduguri a taron sarakunan gargajiya na bakwai an gudanar da shi ne a karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar wanda ya gargadi ‘yan bindigar da ke kisan al’umma a Arewa da kasa bakidaya.
Shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Nijeriya ya bayyana cewar lokaci ne na daukar matakan kawo karshen kalubalen tsaro da ke addabar kasa ba wai tattanawa da gudanar da taruka ba, ya ce Allah zai hukunta dukkanin su da ke rike da matsayi idan har suka bari a na kashe mutane ba gaira ba dalili.
Sarkin Musulmi ya bayyana cewar ba wai sun taru ne domin kamanta kan su da ‘yan siyasa ko hukumomin tsaro ba, illa dai wajibi ne dukkaninsu su hada kai su samar da hanyoyin magance matsalolin.
Ya ce hukumomin tsaro na matukar kokari wajen magance matsalolin tsaro amma akwai bukatar su kara zage damtse wajen sauke nauyin da ke kan su. Ya ce wajibi ne a yi amfani da tattara bayanan sirri su kuma yi aiki da sarakuna domin samar da mafitar magance matsalolin tsaro da kasa ke fuskanta.
A taron mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda ya bude taron ya bayyana cewar gwamnatin tarayya za ta yi aiki da sarakunan gargajiya wajen shawo kan matsalolin tsaro domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Shettima wanda Gwamna Babagana Zulum ya wakilta ya yabawa kokarin jami’an tsaro kan tsaron iyalokin kasa da suke yi tare da kira gare su da su kara daura damarar kawar da matsalar tsaro a fadin kasa bakidaya.
A nasa jawabin a matsayin Gwamna; Zulum ya bayyana cewar kungiyar gwamnoni za ta yi aiki da majalisar kasa domin ganin sarakuna sun samu tanadi a cikin kundin tsarin mulkin kasa domin karfafa masu wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Kafa Majalisar Sarakunan Gargajiya
Wakilnmu ya labarto cewar ita kan ta kungiyar gwamnonin Nijeriya ta bukaci sarakuna su shige kan gaba wajen yaki da ayyukan ta’addanci wanda suka ce wajibi ne a fara shi daga tushe.
Domin cimma wannan manufar, gwamnati ta fara yunkurin tabbatar da dokar kirkiro da Majalisar Sarakunan Gargajiya wadda za ta baiwa sarakunan damar damawa da su a sha’anin gwamnati.
Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma shugaban kwamitin kirkiro da Majalisar Sarakuna, Gwamna Hope Uzodinma ya bayyana cewar kalubalen tsaro da ake fuskanta a yanzu, ya tilasta samun kulawar sarakuna ga wadanda ke nesa da gwamnati da mutanen karkara ta hanyar matakan da ba na amfani da makami ba.
Uzodinma wanda shine gwamnan Jihar Imo ya bayyana cewar bukatar da ke akwai a cikin dokar sarakunan gargajiya ta sanya su a cikin manbobin majalisar tsaro ta kasa da ta jiha muhimmin abu ne wanda ya kamata a ce an yi tun da jimawa.
Ya ce kungiyar gwamnoni ta gudanar da taro da majalisar sarakuna a kan bukatar sanya sarakuna a cikin lamurran gwamnati na al’umma a yankunan karkara da kuma bukatar amfani da taron jin ra’ayoyin jama’a kan gyaran kundin tsarin mulkin kasa domin baiwa sarakuna wani nauyi.
Tuni dai Majalisar Dattawa ta gudanar da karatu na biyu na dokar kafa majalisar sarakunan gargajiya wadda za ta ba su damar sauke babban nauyin al’umma da ke kan su da hannu biyu.
Gwamnati Za Ta Canza Salo – Ribadu
A kokarin kawo karshen gawurtacciyar matsalar tsaro da ta kasa kwarewa, gwamnatin tarayya ta bayyana cewar tuni ta fito da sababbin hanyoyi da manufar kawo karshen matsalar a fadin kasa.
Daga cikin yunkurin akwai ganowa da tarwatsa dukkanin hanyoyin da ake shigowa da makamai masu hadari a cikin kasa kuma suke fadawa a hannun gurbatattu.
Mashawarcin shugaban kasa kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan kwanan baya a Minna, Jihar Neja a wajen taron kaddamar da ofishin yanki na cibiyar kula da kananan makamai ta Arewa ta tsakiya domin magance yawaitar makaman a yankin.
Ribadu wanda shugaban cibiyar, Babatunde Kokomo ya wakilta ya ce yawaitar haramttun kananan makamai ne ke ruruta ayyukan ‘yan bindiga ciki har da ta’addanci, rikice- rikice, garkuwa da mutane, fashi da makami, da rikice-rikicen kabilanci wadanda barazana ne ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp