An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo
Published: 25th, July 2025 GMT
A ranar Juma’a wasu ’yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka uku na Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie a garin Arondizogu, a Ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a Jihar Imo, inda suka kashe aƙalla mutane bakwai.
An samu rahoton cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sun yi ta harbin mutanen yankin a ƙauyukan Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
Waɗanda harin ya rutsa da su, masu shaguna ne da kwastomominsu da kuma masu wucewa.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa majiyarr PUNCH cewa, waɗanda lamarin ya rutsa da su na zaune ne a wuraren shan barasa, wasu kuma suna wasan diraf, a lokacin da ’yan bindigar da ke kan babur suka yi kamar suna wucewa, suka riƙa harbin kowa a wurin.
Majiyar ta ce, “Mutanen da suka mutu suna cikin mashaya daban-daban suna shaye-shaye, wasu kuma mutanen suna harkar kasuwanci da kula da kwastomominsu, sai aka ji ƙarar harbin mutanen da suke zaune a lokacin, kamar yadda nake magana da ku, kusan mutane 12 ne ke kwance ake tsammanin sun mutu, wasu da dama kuma sun samu munanan raunuka saboda gudun neman tsira.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Henry Okoye ya ce mutane bakwai ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata.
Okoye ya ci gaba da cewa, al’amura sun dawo daidai kamar yadda aka saba a ƙauyukan yayin da aka baza jami’an tsaro tare da gudanar da bincike mai zurfi domin gano waɗanda suka aikata kisan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Imo Ndiakunwanta
এছাড়াও পড়ুন:
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa.
“Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA