Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe
Published: 24th, July 2025 GMT
Wani mummunan al’amari ya faru a Ƙaramar Hukumar Fika da ke Jihar Yobe, inda wata mata mai shekara 35, ta kashe mijinta da itace bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu a kan abinci.
Rahotanni sun nuna cewa matar wacce ’yar garin Abba ce, ta ɗauki katon itacen girki ta rafka wa mijinta bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Dungus Abdulsalam, ya ce bayan faruwar lamarin, an sanar da ’yan sanda kuma nan take suka kama wacce ake zargi.
Marigayin ya rasu nan take, kuma ya bar mata biyu da ’ya’ya biyar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Emmanuel Ado, ya ce ya kamata ake ilimantar da ma’aurata domin rage yawaitar cin zarafi a gidajen aure.
Ya buƙaci malamai da shugabannin addini su taimaka wajen faɗakar da jama’a game da illar tashin hankali a gidaje.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Sannan ta ce za a gurfanar da wacce ake zargin a kotu bayan kammala bincike.
SP Dungus, ya tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da an yi adalci a kan lamari.
Har ila yau, ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci aikata laifi ba a kowane mataki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: matar aure Saɓani
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
Daruruwan mazauna kauyen Fegin Mahe da ke yankin Ruwan Bore a karamar hukumar Gusau ta Jihar Zamfara, sun gudanar da zanga-zanga a gaban Gidan Gwamnati da ke Gusau, inda suka bukaci gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa kan kisan gilla da ‘yan bindiga ke yi a yankinsu.
Masu zanga-zangar sun rike takardu masu dauke da rubuce-rubuce kamar su: “Muna bukatar zaman lafiya a yankunanmu” da “Gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka”.
A cewar mazauna kauyen, harin ya faru ne da safiyar ranar Laraba, lokacin da wasu ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka afka wa kauyen, inda suka rika harbin mai-kan-uwa-da-wabi.
Al’ummar yankin sun bayyana harin a matsayin daya daga cikin mafi muni da suka taba fuskanta a ‘yan shekarun nan, wanda ya bar su cikin tsoro da fargaba.
Masu zanga-zangar sun ce manufarsu ita ce jawo hankalin gwamnati kan tabarbarewar tsaro a yankin da kuma bukatar daukar matakin gaggawa don dakile kisan fararen hula da ake ta yi ba kakkautawa.
Sun kuma koka da cewa har yanzu akwai gawarwakin wasu daga cikin mutanen da aka kashe a dajin, amma babu wanda ke iya dauko su saboda tsoron sake fuskantar hari daga hannun ‘yan bindigar.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa ko martani daga gwamnatin jihar ba dangane da harin ko kuma zanga-zangar da aka gudanar.
Daga Aminu Dalhatu