Gwamantin Kasar Siriya Ta Rufe Hanyoyin Shiga BirninSiweida Na Kasar Saboda Ci Gaba Da Bullar Rikici
Published: 24th, July 2025 GMT
Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun rufe hanyoyin zuwa birnin Sweida bayan sake bullar wani tashin hankali
Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin Sweida da ke kudancin kasar tun daga wayewar garin ranar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin.
Ana zaman dar dar a lardin Suwayda da ke kudu maso yammacin kasar Siriya, inda dakarun gwamnati ke ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin tun da safiyar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin ‘yan kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin.
Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun samu nasarar kwace iko da lardin, tare da kafa shingaye na kasa domin raba bangarorin da ke fada da juna bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Sun kuma hana wucewar daidaikun mutane da ayarin motocin sojoji a kusa da lardin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Masu Zuba Jari Na Kasa Da Kasa Sun Gamsu Zuba Jari A Sin Dama Ce Ta Cimma Nasarar More Riba A Nan Gaba
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp