HKI Ta Jefa Boma-Bomai A Kan Asbiti Tilo Da Ya Rage Yake Aiki A Arewacin Gaza
Published: 13th, April 2025 GMT
Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin.
Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan asbitin ne kawai dama yake aiki a arewacin Gaza, kuma a halin yanzu babu wani asbitin da ya rage a yankin.
Labarin ya kara da cewa bayan wadannan hare-hare kan asbitin na Al-Ahli, mutane da dama basu san inda zasu je don samun jinya ba.
Likitan ta kara da cewa kafin hare-hare na safiyar yau Lahadi dai marasa lafiya wadanda aka yankewa kafafu da kuma wadanda suka ji rauni a kai da kuma kirjinsu ne suka fi yawa a cikinsa. Sannan a halin yanzu babu inda zasu je sai wasu kananan asbitoci wadanda basu da kayakin aiki na kula da su. Kuma tuni wasu sun mutu bayan harin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Janar Ali Fadwi: Muna Aiki Tukuru Domin Sabunta Nisan Makamanmu Masu Linzami
Janar Fadwi wanda shi ne mataimakin kwamndan dakarun kare juyin musulunci na Iran ya ce; Muna aiki akan nisan Zangon da makamanmu masu linzmai za su iya kai wa gare shi.
Fadwi wanda ya gabatar da jawabi a yau Alhamis a wurin taron girmama shahidan rundunar dake kula da kare sararin samaniyar Iran, ya kara da cewa; Babu iyaka ko haddi akan aikin da Iran din take yi a fagen kare sararin samaniyarta da kuma samun karfi.
Dangane da batun da makiya suke yi na rage tsawon Zangon da makamai masu linzami za su ci, Fadwi ya ce; Wasu suna yin Magana akan abinda bai shafe su ba, kuma ba su da wata masaniya akan hakan.”
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kuma ce; Muna yin aiki ne da abinda magabatanmu su ka bamu umarni, kuma babu abinda ya dame su da maganar makiya.
An yi bikin girmama shahid Hassan Tahrani Mukaddam wanda shi ne ya assasa kerewa Iran makamai masu linzami.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministocin Harkokin Wajen Iran da Rasha sun Tattauna Gabanin Taron Gwamnonin IAEA November 13, 2025 Iraki: An Fara Sanar Da Sakamakon Farko Na Babban Zaben Da Aka Gudanar November 13, 2025 Kenya: An gano tarin zinari a karkashin kasa da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 November 13, 2025 Gaza: Hamas Ta Nemi Kawo Karshen Kisan Kiyashi Da Lamunce Shigar Da Taimako November 13, 2025 MDD ta yi gargadi game da hadarin yunwa a wasu sassa na duniya November 13, 2025 Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza November 12, 2025 Shugaban Iran Ya Aike Da Wasika Ta Musamman Zuwa Ga Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya November 12, 2025 Gwamntin Nijeriya tace Za ta Kare Sojojinta Da Ke Bakin Aiki November 12, 2025 Iran Da Pakistan Sun yi Kira Da Yin Aiki Tare Don Tunkarar Makiyansu November 12, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Rikicin Yankin November 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci