An kashe mata da yara a sabon harin Filato
Published: 25th, July 2025 GMT
Aƙalla mutum 14; ciki har da mata da ƙananan yara ƙanana ne, suka rasu a wani sabon hari da aka kai a Jihar Filato.
Harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a Gundumar Mangor da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos.
Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a KuduWaɗanda aka kashe suna kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar mako-mako da ke garin Bokkos, lokacin da wasu ’yan bindiga suka buɗe musu wuta.
Wannan hari na zuwa ne wata guda bayan wani hari da aka kai wa wasu ‘yan ɗaurin aure daga Zariya a Jihar Filato, inda aka kashe su.
Ƙungiyar Bokkos Cultural Development Forum (BCDF), ta tabbatar da faruwar harin.
Shugaban ƙungiyar, Farmasum Fuddang, ya ce suna jimami da ɓacin rai saboda wannan hari, musamman ganin cewa an sha gudanar da zaman sulhu tsakanin manoma da makiyaya.
Ya ƙara da cewa mata da ƙananan yara na daga cikin waɗanda suka rasu.
Fuddang, ya danganta harin da wata ƙabila.
Ya kuma ce wata ƙungiyar ta’addanci tana ƙone ƙauyuka da ƙwace gonaki a yankin Mushere.
A cewarsa, burinsu shi ne su mamaye dukkanin Ƙaramar Hukumar Bokkos, wadda ta ke hedikwatar noman dankalin turawa a Najeriya.
Sai dai makiyaya a yankin sun ce ba su da hannu a cikin harin.
Shugaban Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN) na yankin, Saleh Adamu, ya karyata zargin, inda ya bayyana cewa babu wata shaida da ke nuna cewa Fulani ne suka kai harin.
Ya ce ba a kama ko mutum ɗaya daga cikin makiyaya a wajen da harin ya auku ba, kuma ya ce wannan zargi sabon abu ne da bai taɓa faruwa a yankin ba.
Saleh ya ƙara da cewa, “A duk lokacin da wani abu ya faru, jami’an tsaro su kan gudanar da bincike kafin a gano waɗanda suka aikata laifin. Muna Allah-wadai da wannan hari baki ɗaya.
“Kisan mutane marasa laifi ba shi da wani uzuri da za a aminta da shi.”
A halin yanzu, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa dangane da harin ba.
Wakilinmu ya tuntuɓi jami’an hulɗa da jama’a na Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, da na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, amma ba su ce komai ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo
A ranar Juma’a wasu ’yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka uku na Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie a garin Arondizogu, a Ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a Jihar Imo, inda suka kashe aƙalla mutane bakwai.
An samu rahoton cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sun yi ta harbin mutanen yankin a ƙauyukan Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
An kashe mata da yara a sabon harin Filato Sarkin Katsinan Gusau ya rasuWaɗanda harin ya rutsa da su, masu shaguna ne da kwastomominsu da kuma masu wucewa.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa majiyarr PUNCH cewa, waɗanda lamarin ya rutsa da su na zaune ne a wuraren shan barasa, wasu kuma suna wasan diraf, a lokacin da ’yan bindigar da ke kan babur suka yi kamar suna wucewa, suka riƙa harbin kowa a wurin.
Majiyar ta ce, “Mutanen da suka mutu suna cikin mashaya daban-daban suna shaye-shaye, wasu kuma mutanen suna harkar kasuwanci da kula da kwastomominsu, sai aka ji ƙarar harbin mutanen da suke zaune a lokacin, kamar yadda nake magana da ku, kusan mutane 12 ne ke kwance ake tsammanin sun mutu, wasu da dama kuma sun samu munanan raunuka saboda gudun neman tsira.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Henry Okoye ya ce mutane bakwai ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata.
Okoye ya ci gaba da cewa, al’amura sun dawo daidai kamar yadda aka saba a ƙauyukan yayin da aka baza jami’an tsaro tare da gudanar da bincike mai zurfi domin gano waɗanda suka aikata kisan.