Aminiya:
2025-11-02@12:30:17 GMT

Ruwa da iska sun kashe mutum, sun raba sama da 5,000 da muhallansu a Yobe

Published: 24th, July 2025 GMT

Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu.

Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi 48 ne a fadin kananan hukumomin da lamarin ya faru.

Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace

Dr Goje yan kuma ce bala’in ya shafi gidaje 1,264, tare da raba mutum 5,022 da muhallansu.

Shugaban ya kuma ce hukumarsa tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da tallafi ta kasa da kasa ACF tare da tallafi daga ofishin kula da harkokin wajen Jamus (GFFO), sun raba kayan agajin ceton rai ga magidanta 566 a kananan hukumomin Fika da Potiskum da lamarin ya shafa.

Kazalika, kididdigar haɗin gwiwa ta hukumar ta SEMA da ACF suka fitar ta ba da fifiko ga iyalan da wadanda wannan iftila’i ya fi shafa kai tsaye musamman waɗanda suka rasa gidajensu, da kayan masarufi, ko damar samun wani taimakon na tsafta.

Mohammed Liman Kingimi, na kungiyar ACF, ya tabbatar da kudurin kungiyar na kara ba da taimako bisa ga yadda bukatun hakan suka taso.

Ya ce kungiyar na kuma shirye-shiryen kaddamar da tallafin abinci ga magidanta 566 don rage musu radadi.

Dokta Goje ya buqaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata sannan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na kare al’umma masu rauni ta hanyar xaukar matakan gaggawa.

Ya kuma jaddada qudirin hukumar cewa kullum a shirye take wajen gudanar da ayyukanta kamar yadda ya dace.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ruwa da iska

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai October 30, 2025 Manyan Labarai Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar October 30, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15 October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
  • An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara
  • Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC