HausaTv:
2025-07-26@04:43:42 GMT

Amurka: An gabatar da daftarin kudirin sake duba alaka da Afirka ta kudu

Published: 25th, July 2025 GMT

‘Yan majalisar dokokin Amurka sun gabatar da wani kudirin doka da ke ba da shawarar sake duba alakar Amurka da Afirka ta Kudu da kuma kakaba takunkumi a kan  wasu jami’ai da suka ki amincewa da manufofin Amurka na ketare.

Kwamitin harkokin wajen Amurka ya kada kuri’a don aikewa da daftarin kudiri a kan yin nazarin dangantakar Amurka da Afirka ta Kudu” zuwa ga babban zauren majalisar wakilai, inda za a kada kuri’a a kansa.

Wannan matakin na bukatar amincewa daga majalisun wakilai da na dattawa kafin ya zama doka, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

‘Yar majalisar wakilai Ronny Jackson ce ta gabatar da kudirin dokar a watan Afrilun da ya gabata. Tana zargin Afirka ta Kudu da zagon kasa ga muradun Amurka ta hanyar kulla alaka ta kut da kut da Rasha da China, da kuma nuna adawa ga Isra’ila, gami  da kuma gurfanar da ita a gaban kotun kasa da kasa kan batun kisan gilla a a kan al’ummar Palasdinu.

Kudirin ya ba da shawarar yin cikakken nazari kan alakar kasashen biyu da kuma bayyana jami’an gwamnatin Afirka ta Kudu da shugabannin jam’iyyar ANC wadanda suka cancanci a kakaba musu takunkumi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dokokin Isra’ila Ta Kada Kuri’ar Sake Mamaye Yankunan Flasdinawa

Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da karya dokokin kasa da kasa, inda ta fara mamaye yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan da kwarin Jordan!

Majalisar Dokokin yahudawan sahayoniyya ta Knesset ta kada kuri’a kan wani kudirin doka da ba shi da tushe don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila cikakken ikon mallakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma kwarin Jordan. Kuri’ar dai ta samu amincewar ‘yan majalisu 71, yayin da 13 suka nuna adawa da shi. Kungiyar Hamas ta dauki matakin a matsayin maras halacci a doka.

A wani mataki da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin gida da na waje, Majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta kada kuri’ar amincewa da wani kudirin doka da bai taka kara ya karya ba na tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila ikon mallakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma kwarin Jordan, matakin da ya bullo da wani fanni na shari’a da siyasa da ba a taba gani ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Wakilai Ta Nemi Amurka Ta Maido Da Bizar Shekara Biyar Ga ‘Yan Nijeriya
  • Kwankwaso Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Ware Arewacin Nijeriya A Rabon Arzikin Ƙasa
  • Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu
  • Majalisar Dokokin Isra’ila Ta Kada Kuri’ar Sake Mamaye Yankunan Flasdinawa
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 21 Daga Ƙetare
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Iran Ta Zargi Amurka Da HKI Da Wargaza Dokokin Kasa Da Kasa Da Kuma Yarjeniyoyin Kasa Da Kasa
  • Brazil Ta Shiga Yaki Da HKI, Inda Ta Kudurin Anniyar Goyon bayan Afirka Ta Kudu A Kotun ICJ
  • Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa