Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China
Published: 24th, July 2025 GMT
Wani jrigin saman fasinjoji mallakin kasar Rasha da ke dauke da mutum 50 ya yi hatsari a kusa da yankin Amur na kan iyakar kasar China.
Kafar yada labarai ta Sky News ta rawaito cewa jirgin wanda ke dauke da fasinjoji, ciki har da kananan yara biyar da kuma ma’aikatan jirgi su shida, ya fadi ne ranar Alhamis ba tare da ko mutum daya ya rayu ba.
“Ma’aikatan ceto sun gano wasu sassan jirgin na ci da wuta,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito jami’an ceton na cewa.
Reuters ya kuma ce jirgin wanda mallakin kamfanin Angara Airlines ne, ya fadi ne a kusa da Tyndra, wani gari da ke yankin na Amur, bayan hanyar da yake magana da masu kula nda zirga-zirgar jirage a sararin samaniya ta katse.
Kazalika, kamfanin dillancin labaran Rasha na Interfax, ya ce jirgin ya fadi ne a yunkurinsa na sauka a karo na biyu bayan ya kasa sauka a karo na farko a filin jiragen saman a Tyndra.
Kamfanin ya kuma rawaito cewa rashin kyawun yanayin gani ne a lokacin sauka ne ya haddasa hatsarin.
Sai dai bayan faduwar jirgin yak ama da wuta, kuma ana zargin babu ko mutum daya da ya rayu, kamar yadda wani faifan bidiyo a wajen da jirgin ya fadi ya nuna
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, kamfanin na Angara bai kai ga fitar da cikakken bayani kan musabbabin hatsarin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin jirgi Rasha
এছাড়াও পড়ুন:
Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe
Wani mummunan al’amari ya faru a Ƙaramar Hukumar Fika da ke Jihar Yobe, inda wata mata mai shekara 35, ta kashe mijinta da itace bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu a kan abinci.
Rahotanni sun nuna cewa matar wacce ’yar garin Abba ce, ta ɗauki katon itacen girki ta rafka wa mijinta bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu.
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan sama da mutum 100Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Dungus Abdulsalam, ya ce bayan faruwar lamarin, an sanar da ’yan sanda kuma nan take suka kama wacce ake zargi.
Marigayin ya rasu nan take, kuma ya bar mata biyu da ’ya’ya biyar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Emmanuel Ado, ya ce ya kamata ake ilimantar da ma’aurata domin rage yawaitar cin zarafi a gidajen aure.
Ya buƙaci malamai da shugabannin addini su taimaka wajen faɗakar da jama’a game da illar tashin hankali a gidaje.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Sannan ta ce za a gurfanar da wacce ake zargin a kotu bayan kammala bincike.
SP Dungus, ya tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da an yi adalci a kan lamari.
Har ila yau, ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci aikata laifi ba a kowane mataki.