Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)
Published: 25th, July 2025 GMT
Hikimar Rashin Hade Farkon Shekarar Musulunci Da Tarihin Manzancin Annabi (SAW)
Masu karatu har yanzu dai muna kan bayani game da abubuwan da suka sa Sahabbai ba su kafa tarihin kirgen shekarar musulunci ba da wasu manyan alherai na Musulunci, sai suka zabi Muharram ta zama farkon shekarar tare da lakaba mata shekarar Hijirah.
A makon da ya gabata mun yi bayani kan hikimar ware farkon shekarar daga watan Rabi’ul Auwal zuwa watan Muharram saboda girman haihuwar Manzon Allah (SAW). A yau kuma, za mu ci gaba da bayani a kan ware kirgen farkon shekarar daban da ranar da aka fara aiken Manzanci ga Annabi (SAW).
Tun ana sauran shekara uku Manzon Allah (SAW) ya cika shekara 40 da haihuwa, ya rika fita zuwa Halwa (kadaita) a wajen garin Makka a cikin Kogon Hira, mai nisan mil shida daga cikin garin na Makka. Manzon Allah a lokacin ya bar gida, ya bar iyali, ya bar kowa domin ya kadaita da Ubangijinsa.
Wannan Kogon Hirar, lokacin da muka yi Hajji a 2004, mun ziyarci Kogon, muna yin Sallar Asuba muka fito amma ba mu kai ba sai wurin karfe takwas. Ga motoci na wucewa da komai amma kuma saboda dajin wurin ga birori ne suna ta tsalle-tsalle. To, mai karatu ka yi tunani da kwakwalwarka, a 2004 ga wasu namun daji nan har yanzu a wurin, to ina ga in an koma sama da shekara dubu daya da dari biyar, yaya wajen nan ya kasance kenan? Amma haka Annabi (SAW) zai je wajen kuma idan ya tafi ba a kasan dutsen yake zama ba sai ya hau samansa, an bar gari, an bar iyali, an bar dangi, yanzu ma an bar kan kasa ma bakidaya. Shi ma dutsen ba a zauna a sararinsa ba sai da aka shiga kogonsa, Subhanallah! In ka je hanyar shiga Kogon ma za ka ji kana hawaye saboda tafakurrin wadannan abubuwan na Manzon Allah (SAW).
Haka Annabi (SAW) yake zama a cikin Kogon, ya yi wata daya zuwa wata uku har sai abincinsa ya kare. Akwai ruwayar Sayyidina Aliyu (Karramallahu wajhahu) da ya ce idan abincin Manzon Allah ya kare shi yake kai masa. Kuma ya ce tun a wannan lokacin yakan ji wani irin kamshi a wurin wanda babu irinsa a Makka. Haka Manzon Allah ya ci gaba da yi har Hakku ya yi masa tajalli fatahi ya samu. Malaman Tafsiri kuma suka ce har Mala’ika Jibrilu ya zo masa. Ya ce masa “yi karatu”, Manzon Allah ya ce masa “ni ba mai karatu ba ne”, sai da aka yi haka sau uku kafin ayoyin nan na Suratu Ikra’a suka sauka masa (SAW). Daga nan fa sai Duniya ta yi wani irin numfashi, Manzon Allah (SAW) ya fara karantar da mu al’ummarsa da Larabci abubuwan da ya samu daga Ubanginjinsa tare da nuna mana kyawawan dabi’u.
A wannan lokacin da yake zuwa Halwa a Kogon Hira ibada ce ta Tafakkuri yake yi (Malamai sun ce da akwai wani abu da zai fi La’ilaha illallahu, zai zama Tafakkuri ne). Don haka babu wanda zai ce babu Halwa a Musulunci. Idan dai mutum zai nemi sanin hukunce-hukuncen ibada ne, ya tafi wurin Malamai, ba zai samu wannan a Halwa ba. Amma idan zai nemi sanin wani abu mai zurfi ne na Imani to wannan sai da kebancewa (Halwa).
Yanzu mutum ya yi tunani, kafin Manzon Allah (SAW) ya kawo mana addinin nan, sai da ya bar iyali, ya bar gari, ya bar kowa ya tafi kogon dutse ya yi Halwa ta shekara uku, to wani ya zo da rana tsaka ya yi shigar burtu ya ce mana ya san komai na addinin, abin da ya ga dama shi ne mai kyau, wanda bai ga dama ba haramun ne, yaushe hankali zai kama wannan ballantana imani? Ba don Rahamar Manzon Allah da ya ce ya bar mu a hanya mai sauki ba, yaushe addinin zai samu mana. Kuma dai duk da saukin addinin yana da hawa-hawa, Islam, Iman da Ihsan. Don haka ba komai na addini za ka ce ka sani ba, dole akwai iya gejinka na Islam, haka nan a Iman sannan ga kuma Ihsan ba adadi. Wani ma ya ce ba ilimin badini a cikin addini, yanzu Manzon Allah ya zauna ne a gida a gaban mata da yara addinin ya sauka? Ai sai da ya bar gida ya shiga Kogon Dutse ya yi Halwa. Kuma ba Manzon Allah shi kadai ba, sauran Annabawa ma haka ne. Har gara Kogon Hira ma a kusa yake idan aka kwatanta da Dutsen Duri Sina’a, wurin da Annabi Musa (AS) ya yi magana da Allah. Cikin dajin da mutum mai tsoro ba zai iya zuwa ba, ko a yanzu dubi yadda wurin yake balle a wancan lokacin nasu. Dubi Annabi Ibrahim, daga Isra’ila ya dauko mace da danta zai musu gida kawai amma sai da ya shafe wurin mil dubu hudu ya kawosu Makka ya ajiye. Don haka abubuwa na Annabawa da bin hanyarsu ba a sa dan karamin hankalinka a ciki.
Daga wannan Halwar ce Manzon Allah (SAW) ya zo mana da duk alheran da duniya ta sauyu da su. Larabawan da ba su iya karatu da rubutu ba suka zama Malamai. Daulolin da suka zama suna mulkar Larabawan duk suka juya suka zama a karkashinsu, sun samu yalwa na abinci maimakon gurasa da busasshen nama kawai da suke ci a da. Ko a baya-bayan nan ma, shugaban Hadaddiyar Daular Laraba (marigayi) Bin Zayed, ya roki Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya yi musu addu’a saboda kasarsu ba ta da komai na arziki, Shehu ya ba shi Darikar Tijjaniyya ya yi masa addu’a ya ce komai zai zo muku. Su manyan kasar sun san haka kuma wasu har yau suna rike da alkawari.
A shekarar da aka aiko Manzon Allah (SAW), shekarar giwa tana da 40, shekarar haihuwar Annabi Isah kuma tana da 611. Allah ya ba Manzon Allah Alkur’ani wanda sai dai mu dan tsakuri abin da za mu iya a cikinsa, mu dauki zahirinsa da ya yi mana magana a kan hukunce-hukuncen ibadu da sauran mu’amaloli, sai dai mu yi wanka a bakin koginsa kawai, amma fa a Kogon Hira aka debo shi, shekara uku ana Halwa dominsa duk da karfin annabta.
Allah ya ce, wannan Alkur’anin “Littafi ne da aka saukar a gare ka (SAW) don ka fitar da mutane daga cikin duffai (mai yawa), ka shigar da su haske (guda daya) da izinin Ubangijinka (abin ba zai yiwu ba in ba izinin Ubangiji) izuwa tafarkin Mabuwayi abin godiya. Shi ne Allah mai mallakar komai da komai da ke cikin sammai da kasa”. Wannan aya sirrin aiken Manzon Allah (SAW) yana cikinta.
Wannan Alkur’ani shi ne tsarin mulkin da ya shafe kowane irin tsarin mulki duka, shi ne ya tsere wa dukkan sauran littafan da suka zo daga Allah. Ya shafe duk wani tunani na masu falsafa irinsu Aristotle, Karl Mad, da su Bictor Couzen da Khalidr Ruhi, Nepolion, William John, duk Alkur’ani ya shafe su. Haka nan duk wanda ba a cikin Alkur’anin ne zai yi tafakkuri ya fito da abubuwa ba, Alkur’ani ya shafe shi daga nan har tashin kiyama. Don haka mu so Allah, mai rahama ne, mai jinkai ne komai nasa mai sauki ne. Sannan duk mai son komai nasa ya yi dai-dai, ya debo a cikin Alkur’ani.
To duk da wadannan alherai na sirrin aike, Sahabbai sun ajiye kirgen shekarar musulunci ne da Hijirah saboda hikima.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi da kashe yara 2 a Bauchi
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace yara da yin garkuwa da su sannan ta kashe su.
Rundunar ta ce wadannan kananan yara biyu mata ne ‘yan shekara bakwai, lamarin da ya jawo tarzoma da kona coci.
Kakakin Rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya shaida wa manema labarai haka a Bauchi ranar Alhamis.
NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — KwankwasoWakil Ya bayyana cewa an samu rahoton faruwar lamarin ne a ranar 22 ga watan Yulin 2025, da misalin karfe 3:00 na rana.
Ya ce, “Wata matashiya mai shekara 19 mai suna Esther Gambo daga ƙauyen Lemoro da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi ta yaudari wasu yara mata biyu ‘yan shekara bakwai, Khadija Sama’ila da A’isha Dahiru daga ƙauyen Unguwan Sarkin Yaki. Daga bisani Bayan ta shiga dasu daji sai ta sa adda ta kashesu a wat gonar masara.
“Da samun wannan labarin sai ’yan sanda tare da ’yan banga suka bazama neman matar a cikin dajin, kuma sun yi nasarar ƙwato gawarwakin yaran matan da suka rasu, sun kama Esther Gambo, tare da kuɓutar da wata jaririyar da aka yi garkuwa da su,” in ji Wakil.
Kakakin ’Yan Sandan, ya kuma ce binciken farko ya nuna cewa wacce ake zargin Esther Gambo ta lallaɓa ‘yan matan ne da nufin samun sabuwar haihuwa mace da za ta kai wa wata mata mai suna Nafisa Dahiru.
Bayan da ta samu jaririyar, sai Esther ta kai ‘yan matan biyu data sato zuwa gonar masara da ke kusa, inda ta kashe su da adda kafin ta gudu daga wurin.
Wakil ya ce, “Bayan faruwar wannan lamari, tashin hankalin jama’a ya ɓarke, galibi tsakanin matasan Musulmin yankin, wanda ya haifar da mummunar zanga-zanga, ciki har da ƙona coci-coci, da yunƙurin ƙona ofishin ‘yan sanda da ke Garin Tulu.
“Sai da aka tura ƙarin jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sandan yankin Toro da kuma sassan da ke maƙwabtaka da su domin dawo da zaman lafiya, inda suka yi nasarar daƙile tarzomar. A sakamakon wannan tashin hankalin, an kama mutum 16 da ake zargi da hannu a cikin lamarin.
“Wadanda ake zargin da aka kama su ne Abbas Abdullahi mai shekaru 20, Mubarak Auwal mai shekaru 19, Abdullahi Muhammad DA Ake kira P.A), mai shekaru 19, Dauda Abdullahi mai shekaru 19, Abubakar Sama’ila, mai shekaru 18, Ibrahim, Auwal mai shekaru 18, Abdulmutallib mai shekaru 18 Abdulrahman Ibrahim, mai shekaru 17.
“Sauran wadanda ake tuhuma sun hada da Abdulwahid Sulaiman, mai shekaru 17, Salihu Shuaibu, mai shekaru 20 , Sirajo Halliru, mai shekaru 24, Musayib Abdullahi, mai shekaru 21 , Ibrahim Abubakar , 19 , Esther Idi, 19, Gambo Yakubu, Mai Shekaru 20 da Idi Bitrus, Mai Shekaru 50,” in ji Kakakin.
Wakil ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya jaddada muhimmancin kiyaye doka da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar Bauchi.
Ya nuna damuwarsa kan ayyukan baya-bayan nan da ke kawo cikas ga bin ƙa’idojin shari’a tare da yin kira ga al’umma da su guji daukar doka a hannunsu.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa ana gudanar da cikakken bincike tare da kiran da kowa ya kwantar da hankalinsa domin an shawo kan lamarin yadda ya kamata.