Aminiya:
2025-07-25@23:11:01 GMT

Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso

Published: 25th, July 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali wajen gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen taron bana kan shawarwari na masu ruwa da tsaki a Jihar Kano.

Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71

A cewarsam Tinubu ya yi watsi da halin da yankin arewacin ƙasar ke ciki wajen gina Kudancin Najeriya da kuma samar musu da kayan more rayuwa.

“Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan,” in ji Kwankwaso.

Kwankwaso wanda ya yi wa jam’iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023, ya zargi jam’iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Nijeriya.

Ya ce: “Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi,” in ji Kwankwaso.

Ya ce wannan ya sa ake fama da rashin tsaro da talauci da sauransu.

Kwankwaso ya ce yawancin hanyoyi da ke Arewacin suna cikin mawuyacin hali, wasu ma sun lalace, yayin da gwamnatin APC ke ci gaba da ware maƙudan kuɗaɗe wa ɓangaren ayyukan more rayuwa a Kudancin ƙasar.

Ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sauya alƙibla domin tafiya da kowa da kuma tabbatar da cewa an raba albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin ci gaban dukkan sassan ƙasar.

“Yanzu lokaci ne da ya kamata gwamnati ta kawo sauyi, domin mu san cewa ba gwamnati ce kaɗai ta wani ɓangare guda ba,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Rabi u Musa Kwankwaso

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya sake miƙa buƙatar karɓo bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dokokin Tarayya buƙatar ƙara ranto bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare, ƙarƙashin shirin ciyo bashin na gwamnatin tarayyar na 2025 zuwa 2026.

Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Tinubu ya aikewa majalisar, wadda Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya karanto a zamansu na yau Laraba.

Dalilin da muka gaza biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi — Gwamnatin Borno WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya

Takartar ta ambato shugaban ƙasar na cewa karɓar rancen ya zama tilas saboda buƙatar ƙarin kuɗi da aka yi a aikin babbar hanyar Lagos zuwa Calabar, wanda ya tashi daga Dala miliyan 700 zuwa Dala miliyan 747 — ƙarin Dala miliyan 47 ke nan.

Idan ba a manta ba, a jiya Talata ne Majalisar Datttawan Nijeriya ta sahale wa shugaba Tinubu karɓo bashin Dala biliyan 21 daga ƙetare domin cike giɓin kasafin kuɗin kasar na bana zuwa baɗi.

Ko a watan Nuwambar 2023, majalisar wakilai da ta dattawa sun amince da ciyo bashin Dala biliyan 7 da miliyan 800, da kuma Euro miliyan 100 domin gudanar da manyan ayyuka da sauran ayyukan raya ƙasa.

Kazalika, a watan Maris ɗin 2025 ma majalisar ta amince Tinubu ya ciyo bashin Dala biliyan 21 da miliyan 500 daga ƙetare, da kuma karɓar takardun kuɗin banki da suka kai Naira biliyan 757 da miliyan 900 domin biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu.

Ya zuwa watan Maris dai, adadin bashin da ake bin Najeriya ya kai Dala biliyan 91 kwatankwacin Naira tiriliyan 121, a cewar wani rahoton ofishin kula da basuka na ƙasar DMO.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 3.5 Wajen Gina Shaguna A Farm Centre
  • Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Gusau
  • HOTUNA: Yadda Kwankwaso ya karɓi ’yan APC zuwa NNPP a Kano
  • Kwankwaso Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Ware Arewacin Nijeriya A Rabon Arzikin Ƙasa
  • Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu
  • ‘Yan Nijeriya Miliyan 40 Ke Fuskantar Barazanar Kwararowar Hamada – Ministan Muhalli
  • Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar
  • Tinubu ya sake miƙa buƙatar karɓo bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare
  • WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya