Brazil Ta Shiga Yaki Da HKI, Inda Ta Kudurin Anniyar Goyon bayan Afirka Ta Kudu A Kotun ICJ
Published: 24th, July 2025 GMT
Gwamnatin kasar Brazil tana shirin bayyana goyon bayanta ga Afirka ta kudu a karar da ta shigar a gaban kotun ICJ dangane da tuhumar jami’an gwamnatin HKI da aikaya kisan kiyashi a Gaza.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wata jaridar kasar Brazil Folha De S tana fadar haka. Sannan kamfanin dillancin labaran reuters ya tabbatar da labarin a jiya Laraba.
A shekara ta 2023 ne gwamnatin Afirka ta kudu ta shigar da karar don tabbatar da cewa gwamnatin HKI ta na aikata kissan kare dangi kan kasar Amurka. Wanda ya sabawa dokar hana kissan kare dangi ta MDD ta shekara 1948.
Sannan a cikin watan Octoban da ya gabata ne, Pretoria ta gabatar da shaidu da bayanai da suke tabbatar da ikrarinta a gaban alkalan kotun a birnin Hague cibiyar kotun. Wannan ya sa kotun ta fidda sammacin kama firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da kuma ministansa na yaki a lokacin Aut galant.
Kasashen duniya da dama sun amince da sammacin, sun kuma dauki alkawalin kama so a duk lokacinda suka kuskura suka shiga kasashensu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Hukumar Hisba Ta Jihar Jigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta kafa Hukumar Hisba a matsayin hukuma ta dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na gwamnan Hamisu Muhammad Gumel ya fitar ga manema labarai a Jigawa.
Sanarwar ta bayyana cewa bikin sanya hannun ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnati dake Dutse, inda manyan jami’an gwamnati suka halarta, ciki har da Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Sani Isyaku.
Ta ce Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma, bayan kai-komo na sama da watanni takwas da bangaren majalisar dokoki da majalisar zartarwa suka yi domin kaiwa ga gaci.
“Yau mun kammala aikin da muka fara kusan watanni bakwai zuwa takwas da suka gabata. Da ikon Allah, an kammala kudurin da ya kafa hukumar Hisba a matsayin cikkakiyar hukuma a Jihar Jigawa,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya yi wa hukumar fatan alkhairi, tare da fatan za ta kawo ƙarin daidaito da tarbiyya a cikin al’umma.
Ya kuma shawarci ma’aikatan Hisba da su kasance masu tsoron Allah, adalci da kuma jajircewa a yayin gudanar da aikinsu.
Gwamna Namadi ya yaba wa kwamitin da ya shirya kudurin bisa himma da sadaukarwa wajen kammala wannan aiki mai muhimmanci.
Bayan sanya hannu kan wannan doka, yanzu hukumar Hisba ta samu cikakken iko na gudanar da aikinta a duk fadin Jihar Jigawa bisa tsarin da aka shimfiɗa na inganta tarbiyya, adalci da walwalar al’umma.
Usman Muhammad Zaria