Sanatocin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar ‘Yan Wasan Kano
Published: 1st, June 2025 GMT
Sanatocin Arewa sun bayyana alhini da jimami kan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin ‘yan wasan Jihar Kano da ke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala a Jihar Ogun.
A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Musa Yar’adua ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da kuma Gwamnatin Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya.
Sanata Yar’adua ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu, ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa. Ya buƙaci Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) da ta gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar hatsarin.
Ya kuma roki Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya ɗauki matakin karrama waɗannan ‘yan wasa da masu horar da su ta hanyar sanya sunayensu a kan wasu muhimman wuraren jama’a ko filayen wasa domin girmama gudummawar da suka bayar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Arewa
এছাড়াও পড়ুন:
Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma’a – Gwamnati
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Ali Haruna Makoda, ya buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci.
Ya yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da ya makara wajen dawowa makaranta zai iya fuskantar hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp