Shugaba Tinubu ya zanta da manema labarai bayan kammala Sallar Idi na karshen watan Ramadan a filin da aka gabatar da Sallar Idi na kasa a Abuja ranar Lahadi.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su koma kan aikata abubuwan da su ba ta dace ba, a maimakon haka, ya bukace su da su dage wajen aiwatar da kyawawan dabi’un game da darusan da suka koya a watan Ramadan.

A cikin hudubar da babban limamin masallacin kasa dake Abuja, Dakta Abdulkadir Salman Sholagberu, wanda ya jagoranci Sallar ya gabatar, ya jaddada bukatar Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadar da suka koya a Azumin watan Ramadan, wanda ya hada da koyar da rayuwar soyayya, hadin kai cikin adalci, kula da gajiyayyu da marasa galihu.

Ya jaddada cewa ya zama wajibi a ci gaba da gudanar da rayuwar ibada da tsarki da kuma biyayya ga Allah ko da a bayan Ramadan.

Dakta Salman ya bukaci al’ummar Musulmi da su zauna lafiya, da lumana, da kaunar kasa, ba tare da nuna wariya ba.

A gefe guda kuma, kungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN ta mika sakon taya murna ga al’ummar Musulmin Nijeriya a daidai lokacin da suke gudanar da bukukuwan karamar Sallah, yayin da a lokaci guda ta bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki mummunan kisan gillar da aka yi wa mafarauta 16 a garin Uromi na jihar Edo.

A cikin sakon taya murna bayan kammala azumin watan Ramadan, shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya jaddada muhimmancin bikin Idin karamar Sallah a matsayin lokacin tunani, da yin addu’a ga al’umma.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa a jiya ne Shugaba Tinubu ya gudanat da bikin Sallah na farko a Abuja tun shekarar 2023.

Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, Babban Mai Bai Wa Shugaban kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Nuhu Ribadu, da wakilan majalisar zartarwa ta tarayya, da sauran manyan jami’an gwamnati sun halarci Sallar.

A nasa bangaren, shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya taya al’ummar Musulmi barka da sallah, inda ya bukace su da su yi addu’ar samun hadin kan al’umma.

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Hon. Eseme Eyiboh, Akpabio ya jaddada muhimmancin hadin kai tare da karfafa gwiwar Musulmi da su ci gaba da hadin kan kasa.

Hakazalika, gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya taya al’ummar Musulmin jihar da ma kasar murnar bukukuwan karamar Sallah.

A sakonsa na fatan alheri, mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Yinka Oyebode, a ranar Lahadin da ta gabata, gwamnan ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin kwanaki 30 tare da jaddada bukatar ci gaba da gudanar da ayyukan ibada da ake nunawa a watan Ramadan duk shekara.

Gwamna Oyebanji ya hori al’ummar Musulmi da su rika amfani da koyarwar wata mai alfarma a duk wani aiki da za su gudanar, inda ya bukace su da mabiya sauran addinai su ci gaba da zama cikin soyayya da zaman lafiya da juna a matsayin ‘yan’uwa.

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi kira ga al’ummar jihar da su amfani da darasin da suka koya a cikin watan Azumin Ramadan, sannan su rungumi zaman lafiya da hadin kai.

Gwamnan, a wani jawabi da ya yi a ranar Lahadin da ta gabata jim kadan bayan Sallar Idin, ya taya al’ummar Musulmi murnar Sallah, a karshen Azumin watan Ramadan.

Ya bukaci al’ummar Musulmin Jihar Zamfara da sauran kasashen duniya da su yi zurfafa tunani kan sadaukar da kai ga Allah kamar yadda aka yi a cikin watan Ramadan.

Hakazalika, gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Yusuf, ya bukaci al’ummar Musulmi da su kiyaye dabi’u na hakuri, tausayi, hadin kai da aka koyar a cikin watan Ramadan.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature, ya fitar, ya jaddada muhimmancin sadaukarwa, tare da karfafa gwiwar ‘yan kasa da su tallafa wa marasa galihu da kuma samar da zaman lafiya a cikin al’ummarsu.

PDP, Atiku da Obi sun bukaci ‘yan Nijeriya da shugabanni su ji tsoron Allah da tausayi a tsakaninsu

Jam’iyyar PDP, Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, sun taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan mai alfarma, sun kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su kwatanta irin darusan da suka koya, kyawawaan dabi’un soyayya, hadin kai, zaman lafiya, hakuri, kamewa da kuma mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki da sauran kyawawan dabi’u da suka shafi gudanar da mu’amalarsu ta yau da kullum.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Hon Debo Ologungaba ya fitar, PDP ta bukaci ‘yan Nijeriya musamman masu rike da madafun iko a dukkan matakai da su sake sadaukar da kansu wajen gudanar da ayyukansu na nuna son jama’a bisa kyakkawan jagoranci, gaskiya, da rashin nuna wariya a dukkan ayyukansu tare da kawar da ayyukan cin hanci da rashawa, girman kai, magudi, da kaucewa nuna rashin sanin halin da al’umma ke ciki.

Mai magana da yawun babbar jam’iyyar adawar ya ce jam’iyyar ta damu matuka da yadda ‘yan kasar ke gudanar da bukukuwan Sallar Idi cikin hali na damuwa saboda wahalhalun da ba za a iya jure su ba na rashin kyawun mulkin jam’iyyar APC, wanda ya kara dagula al’amura a kasar cikin shekaru biyu da suka wuce.

Hakazalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a shekarar 2023, Mista Peter Obi, ya mika sakon fatan alheri ga Musulman Nijeriya, inda ya bukace su da su zama mdabbaka irin darusan da suka koya a Ramadan shi zai jagoranci rayuwarsu ta yau da kullum.

Mai magana da yawun Peter Obi, Mista Ibrahim Umar, ne ya mika sakon fatan alherin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Obi a cikin sakon nasa ya ce, “Addu’armu itace Allah Madaukakin Sarki Ya karbi addu’o’inmu da azuminmu a yanzu da kuma ko da yaushe.

“Hakika abin farin ciki ne a gare ni in yi buda-bakin Azumin watan Ramadan tare da al’ummar Musulmi daban-daban a fadin kasar nan, samun albarkarmu da jin dadin junanmu ba wai kawai watan Ramadan kadai ba, har ma ya zama wani bangare na rayuwarmu ta yau da kullum.”

Ya yi addu’ar Allah ya sanya albarka a darusan da aka koya a watan Ramadan, wanda yin hakan shi zai sanya “soyayya a zukatanmu, zaman lafiya da hadin kai za su bunkasa a cikin al’ummarmu.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Matsin Rayuwa ya taya al ummar Musulmi cikin wata sanarwa da Azumin watan Ramadan al ummar Musulmi da ya bukace su da da suka koya a zaman lafiya A cikin wata a cikin wata yan Nijeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kakkausar suka ga harin da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan, inda ta bukaci kasashen Larabawa da na musulmi da su dauki matsaya daya kan matakan wuce gona da iri na gwamnatin mamayar.

Basem Naim, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas,ne  ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, yayin da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen musulmi suka halarci taron gaggawa na Doha, domin tattauna harin da Isra’ila ta kai kan shugabannin Hamas a kasar Qatar.

Babban jami’in na Hamas ya yi kira ga shugabannin yankin da ke halartar taron da su mayar da Isra’ila saniyar ware a siyasance da ta fuskar tattalin arziki da kuma gurfanar da jami’an Isra’ila a kotunan duniya domin kawo karshen yakin kisan kare dangi a Gaza.

Naim ya kuma jaddada cewa, harin da Isra’ila ta kai kan tawagar Hamas a birnin Doha, ya zo ne a daidai lokacin da tawagar ke tantance wata sabuwar shawarar tsagaita bude wuta a Gaza.

“Mun nuna sassauci mafi girma na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza, amma sojojin mamaya ne, ta hanyar amfani da kisa da kuma sanya sharuddan nasu, ke kawo cikas ga duk wata yarjejeniya da za a iya cimma.”

Daga karshe ya bayyana cewa kungiyar Hamas tana sa ran taron zai dauki matsaya guda daya mai ma’ana tsakanin Larabawa da musulmi, da suka hada da tsagaita bude wuta nan take da kawo karshen yakin Gaza, da dage shingen da aka yi, da yanke duk wata alaka da Isra’ila, da gurfanar da isra’ila kan laifuffukan da ta aikata, da samar da falasdinu mai  ‘yancin cin gashin kai, da Al-Quds a matsayin babban birninta, da kuma tabbatar da ‘yancin komawar ‘yan gudun hijira.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya September 14, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Rashin Halarta Tawagarta A Kada Kuri’a Kan Batun Falasdinu   September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
  • Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila