Karamar Hukumar Jahun Ta Bada Tallafin Noman Rani Ga Manoma 300
Published: 29th, March 2025 GMT
Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300.
A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma.
A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu.
Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani.
Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso 60 cikin 100, yayin da zasu dawowa da gwamnati kaso arba’in kacal 40.
A nasa jawabin, jami’in kula da noman rani Malam Suraja Dahiru ya ce gwamnatin Jihar Jigawa ta bada umarnin baiwa matasa filin noma a kalla kadada 100 a kowacce karamar hukuma.
Ya yi nuni da cewar, shugaban karamar Hukumar Jahun ne kadai ya kara adadin filin noma zuwa dari uku.
Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, kayayyakin tallafin da aka raba sun hada da Injin ban ruwa da takin zamani buhu bakwai da irin shuka na shinkafa buhu daya da injin feshi da maganin kwari da sauran kayan aikin gona.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Jahun Noman Rani
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin
Da yake la’antar kisan a matsayin “mummuna, dabbanci, kuma lamarin da ba za a lamunta ba,” gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da adalci. Ya umurci hukumomin tsaro da su dau mataki tare da kama wadanda ke da hannu a kisan nasa nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp