Leadership News Hausa:
2025-09-18@00:43:28 GMT

Bukatar Hukunta Masu Jagorantar Kashe-kashe A Nijeriya

Published: 25th, July 2025 GMT

Bukatar Hukunta Masu Jagorantar Kashe-kashe A Nijeriya

Koda ya ke dai, a lokacin ‘yansanda sun yi nisa ban gudanar bincike, amma babu wanda suka iya kamawa, kuma ba a kara shigar da wata sabuwar kara a gaban kotu ba, duk tsawon wadannan shekarun.

Wannan bukatar da Muyiwa ya biro da ita, tamkar bude wani sabon babi ne, kan batun hallaka manyan mutane a kasar, wadda za a iya cewa, tun daga 1999, har zuwa yau, amma shiru ake ji, kan daukar wani kwakwaran mataki.

A wani taro a kwanan baya, babban Lauya SAN Cif Kanu Agabi, ya bijiro da zargin yadda ake gaza hukunta masu aikata manyan laifuka a kasar, inda kuma ake samun dogon jan kafa, kan shari’ar da ta shafi, marasa karfi a kasar.

Wannan zargin na Kanu, ya nuna a zahiri, yadda aka yiwa bangaren shari’ar kasar, rikon Sakainar Kashi, musamman wajen gaza cafko, masu aikata manyan laifuka, domin su fuskanci hunci.

Bugu da kari, a kasidar da ya gabatar a a taron jamia’r NOUN, tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa, yin gaskiya wanzar da zaman lafiya tabbatar da tsaro, tare da bai wa ko wanne dan kasa hakkinsa, su ne, ginshikin da ke bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sai abin dubi a nan, wannan yawabin na, Cif Olusegun, ya kasance yana cin karo da juna, domin a lokacin yana kan Karagar shugabancin kasar ne, aka kashe marigayi Ige.

Cafko irin wadannan masu halka manyan mutane a kasar domin a hukunta su, kamar yadda dokar kasa ta tanada, ba wai kawai hakan zai samar da salama ga ahalinsu bane, musamman duba da yadda suka yi babban rashi, amma hakan zai kuma zama wani babban abin ci gaba, ga kasar.

Kazalka, kamo su din, zai zama tamkar wani gargadi ne, da zai nuna cewa, akwai hukuncin da kasar ta tanadar, ga masu aikata irin wannan halin na rashin imani.

A nan, wannan Jaridar, ta yi waiwaye kan kisan rashin imani da aka akatawa mataimakin shugaban PDP na shiyyar Kudu Maso Kudu Cif Aminasoari Kala (A.K) Dikibo shekaru 21 da suka gabata.

Abin takaici, an hallaka shi ne, da tsayiyar rana a kan wata babbar hanya, a ranar ga 4 Fabiraurun 2004.

Sai dai, har zuwa yanzu, babu wani kokari da rundunar ‘yansanda ko hukumar DSS suka yi, na bankado makasan.

Kazalika, tshohon mataimakin shugaba na Kudu Maso Kudu, rusasshiyar jami’iyyar ANPP Marshal Sokari Harry, an kashe shi a Abuja a ranar 5 ga watan Maris na 2003 a lokacin zaben shugaban kasa

Hakazalika, an yiwa dan siyasa Anthony Olufunsho Williams, kisan gilla a gidansa da ke a rukunin gidaje na Dolphin, a jihar da ke Ikoyi, Legas, a ranar 27 ga watan Julin 2005.

An hallaka shi ne, yayin da ake shirin tsayar da shi, dan takarar gwamna a PDP na jihar Legas.

Rashin daukar matakin, na kara zubur da kimar Nijeriya a idon duniya.

Hakazalika, hakan ya sanya, wasu hukumomin a jihohin kasar nan, ke shawartar alumomin, da su dauki matakan kare kansu, daga hare-haren da aka kai wa jama’a, wanda hakan karara, ya nuna gazawar gwamnatin kasar, na kare rayuka da kuma dukiyoyin ‘yan kasar.

A saboda haka, akwai bukatar, a yiwa bangaren shari’a na kasar garanbawul, domin a lalubo da mafita kan lamarin.

Ko da yake dai, majalisar kasa na kan yunkurin sabunta dokar zabe ta 2022.

A matsayin mu a wannan Jaridar, mun kasance kan gaba wajen yin kira da a samar da sauye-sauye a bangaren shari’a, musamman domin a dawo da kimar da bangaren yake da shi, kamar yadda aka san shi, a shekarun baya.

A tunanin mu, samar da wannan sauye-sauyen a bangaren shari’ar, za a samar da kyakyawan yanayi a bangaren na shari’a, tare da gaggawar daukar makai, kan irin wannan kisan gillar da ake yiwa manyan kasar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: a bangaren shari a

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato

KADA ta yi gargaɗi cewa haƙurin jama’a ya ƙare, tana mai jaddada cewa shiru da halin ko-in-kula daga shugabanni ba za a ƙara yarda da shi ba. Sun yi kira da a tabbatar da adalci da kuma mayar da zaman lafiya a yankin, tare da nuna goyon baya ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Garga.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Burkina Faso: Masu Ikirarin Jihadi Sun Kashe Fararen Hula 50 A Cikin Watanni Hudu
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato