Ministan Lafiya Na Kamaru: Hadin-Gwiwa Ta Fuskar Kiwon Lafiya Ta Shaida Zumunci Mai Karfi Tsakanin Kamaru Da Sin
Published: 24th, July 2025 GMT
Ministan lafiya na kasar Kamaru, Manaouda Malachie ya bayyana jiya Talata 22 ga wata a Yaounde cewa, hadin-gwiwar Kamaru da Sin a bangaren kiwon lafiya ta haifar da babban alfanu ga jama’ar Kamaru, kana alama ce dake shaida dangantakar kut da kut gami da dadadden zumunci tsakanin jama’ar kasashen biyu.
A wajen bikin cika shekaru 50 da kaddamar da hadin-gwiwar Sin da Kamaru ta fuskar kiwon lafiya wanda aka yi a jiya Talata a birnin Yaounde, minista Malachie ya gabatar da jawabi yana mai cewa, hadin-gwiwar kasashen biyu ta fuskar kiwon lafiya ta shaida cewa, kwalliya za ta iya biyan kudin sabulu, idan aka raya hulda mai aminci, da sahihanci kuma bisa muradu iri daya tsakanin kasa da kasa.
Gwamna Sule Ya Ƙara Musanta Zargin Kare Ƴan Ta’adda A Nasarawa Har Yanzu Yaƙi Da Ta’addanci Ne Babban Muradin Gwamnatina — TinubuBabbar jami’a a ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Kamaru, Chen Ya’ou ta bayyana nasarorin da tawagar ma’aikatan lafiyar kasar Sin ta samu a kasar ta Kamaru cikin shekaru 50 da suka gabata.
Rahotannin sun ruwaito cewa, tun daga shekara ta 1975, zuwa yanzu, Sin ta tura tawagogin ma’aikatan lafiya guda 24 zuwa Kamaru, dake kunshe da mutane 786 gaba daya, wadanda suka samar da hidimomin jinya tare da samun babban yabo daga jama’ar kasar. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti.
An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa.
Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a YobeMajiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin yankunan da lamarin ya fi ƙamari, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gaggawa na kiwon lafiya.
Kwamishinan lafiya a matakin farko, Dakta Ibrahim Dangana, ya tabbatar da ɓullar cutar, ya kuma ce jihar ta ɗauki matakai da dama domin daƙile yaɗuwar cutar.
A cewarsa, an kafa cibiyoyin kula da lafiya da killace marasa lafiyan a kowace ƙaramar hukumar da abin ya shafa.
Dangana ya ce “Mun kafa cibiyoyin kulawa da killace masu jinya don rage yaɗuwar cutar, kuma muna kuma wayar da kan jama’a kan cutar,” in ji Dangana.
Ya ƙara da cewa, “Shirin wayar da kan jama’a ya shafi Ƙungiyoyin addini irin su Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), kungiyoyin Islama, da masarautu takwas da ke jihar”.
Domin ƙarfafa ƙoƙarin hana yaɗuwar cutar, gwamnatin jihar ta buɗe cibiyar killacewa a tsohon reshen cibiyar kula da lafiya na matakin farko na Marigayi Sanata Idris Ibrahim Kuta daura da tsohon titin filin jirgin sama a Minna.