Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace
Published: 24th, July 2025 GMT
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Ƙananan Hukumomin Rijau da Mariga a Jihar Neja.
’Yan ta’addan sun fito ne daga Jihar Zamfara, yayin da suke tafiya a kan babura ɗauke da muggan makamai.
Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan mutum sama da 100 Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasaSojoji tare da taimakon jiragen yaƙi na sama sun kai farmaki bayan samun bayanan sirri.
Aƙalla ’yan ta’adda 95 aka kashe a yayin artabun.
Sojojin sun kuma lalata babura 18 tare da ƙwato bindigogi kirar AK-47.
Sai dai an yi rashin sa’a soja guda ɗaya ya rasa ransa a yayin fafatawar.
Dakarun sun sake kai wani farmaki na biyu inda suka ƙwato makamai da yawa tare da tarwatsa ’yan ta’addan.
Jama’a daga Warari, Rijau, da wasu ƙauyuka sun yi murnar nasarar sojojin suka samu.
Da yawa daga cikin mazauna yankunan sun tsere daga gidajensu saboda tsoro, amma sun dawo bayan ganin ƙoƙarin da sojoji suka yi.
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, an ga yadda jama’a ke taya sojoji murna da godiya.
Wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa farmakin sojojin ya daƙile shirin kai hare-hare da ’yan ta’addan suka yi.
Wani mazaunin yankin shi ma ya ce ’yan ta’addan na shirin kai hari wasu ƙauyuka a Mariga, amma sun gudu bayan farmakin sojoji.
An kama tsohon kansila kan iƙirarin mallakar shanuA gefe guda kuma, jami’an tsaro sun kama tsohon kansilan Rijau, Mamman Wazo, bisa zargin iƙirarin mallakar shanun da aka ƙwato daga hannun ‘yan ta’adda.
Wata ƙungiyar sa-kai ce ta kama shi tare da abokin aikinsa, kuma aka miƙa su ga ’yan sanda.
’Yan sanda sun ce an samu shanun ne daga yankin Rijau bayan wasu hare-hare da aka kai.
Sojoji sun ceto mutum 138 da aka saceA wani samame na daban daban, sojoji sun ceto mutum 138 da aka sace a Jihohin Zamfara, Borno, da Adamawa.
Mafi yawan waɗanda aka ceto mata da ƙananan yara ne.
An kuma kama wasu mutane da ake zargin suna taimaka wa ‘yan ta’adda da kayan aiki.
A Jihohin Borno da Adamawa kuma, sojoji sun kama abubuwan fashewa da sauran makamai yayin da suka daƙile wasu hare-haren ’yan ta’addan.
Rundunar sojin ta ce za ta ci gaba da kasancewa cikin shiri don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sojoji sun gode wa al’umma bisa goyon bayan da suke bayarwa, kuma sun buƙaci mutane su ci gaba da bai wa hukumomi bayanai masu amfani.
Sun tabbatar da cewa za su ci gaba da kare ƙasar nan daga barazanar ta’addanci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Adamawa Artabu dakaru Farmaki yaƙi Zamfara yan ta addan yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu Mahara Sun Sake Kashe Mutum 14 A Wani Kauyen Jihar Filato
Shugaban ƙungiyar ya ce harin ya faruwa a dai-dai lokacin da ake kokarin samar da zaman lafiya da sulhu, inda ya bayyana harin a matsayin abin Allah-waɗai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp