Kwanan nan, darektar zartaswa ta hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD, Anacláudia Rossbach, ta yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a hedkwatar hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD dake Nairobi, babban birnin Kenya.

Yayin da aka ambato sakamakon da ya fi jawo hankali da Sin ta samu yayin kyautata kauyuka zuwa matsayin birane da garuruwa, Rossbach ta bayyana cewa, Sin ta cimma nasarar kawar da talauci ga mutane miliyan 800, da kuma tafiya a kan hanyar kyautata kauyuka zuwa birane da garuruwa, kuma wannan darasi ne da ya cancanci kasashen Afirka wadanda suke fuskantar kalubalen kyautata kauyuka zuwa birane su yi koyi da shi.

Ta ce, nan da shekaru 25 masu zuwa, mutane kusan miliayn 800 na kasashen Afirka da na Latin Amurka za su yi kaura zuwa birane, kuma kasashen Asiya da dama su ma suna fuskantar kalubalen fama da talauci. A cewarta, birane na da muhimmanci sosai wajen kawar da talauci, kuma ba ma kawai ya kamata a ba da wurin kwana ga mutane a cikin birane ba, har ma ya dace a ba su damammakin samun ilmi, da guraben ayyukan yi da sauransu, da kuma samun hidimomin kiwon lafiya don kiyaye koshin lafiyarsu, kana ta ce, wannan shi ne muhimmin abun da za mu ci gaba da gudanarwa da kuma tattaunawa a kai. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: zuwa birane

এছাড়াও পড়ুন:

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

 

Tsofaffin shugabannin da suka rasu bayan kammala wa’adinsu

Nnamdi Azikiwe

An haife shi a ranar 16 ga Nuwamba, 1904, Dakta Nnamdi Azikiwe, wanda aka fi sani da “Zik of Africa,” fitaccen dan siyasar Nijeriya ne kuma mai kishin kasa wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samun ‘yancin kai. Ya zama shugaban kasa na farko a Nijeriya daga 1963 zuwa 1966, bayan ya zama Gwamna-Janar a 1960 tare da Firai Minista Abubakar Tafawa Balewa.

Azikiwe ya rasu yana da shekaru 91 a duniya a ranar 11 ga Mayu, 1996, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nijeriya, Enugu, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Bayan shugabancinsa, Dakta Azikiwe ya kasance dan jarida na farko, haziki, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa kishin kasa a Nijeriya a wannan zamani. Ya taka rawar gani wajen kafa jaridu da dama da ke fafutukar neman yancin kai da Pan-Africanism.

Ya kasance mai cikakken imani da ilimi, ya taimaka wajen kafa harsashin karatu a Nijeriya, ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen kafa jami’ar Nijeriya ta Nsukka, inda daga bisani ya zama shugaban jami’ar. Tasirinsa ya wuce siyasa, wanda hakan ya sa aka girmama shi a duk fadin Afirka a matsayin alamar hadin kai da ci gaba.

 

Shehu Shagari

Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, zababben shugaban Nijeriya mai cikakken iko na farko a Nijeriya, ya rasu ne a ranar 28 ga watan Disamba, 2018, a Asibitin kasa da ke Abuja yana da shekaru 93. Ya rike mukamin shugaban kasa daga 1979 zuwa 1983 a karkashin tutar jam’iyyar NPN, har zuwa lokacin da aka hambarar da gwamnatinsa a juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 31 ga Disamba, 1983, wanda Muhammadu Buhari da ya rasu kwanan nan ya jagoranta.

Shagari ya fara tafiyar siyasarsa ne a shekarar 1951 a matsayin sakataren jam’iyyar NPC ta Arewa a Sakkwato. A tsawon shekaru, ya rike mukamai da dama a Jamhuriya ta farko ta Nijeriya. A shekarar 1958, an nada shi Sakataren Majalisar, sannan ya zama Ministan Kasuwanci da Masana’antu na Tarayya.

A tsakanin shekarar 1959 zuwa 1960 ya zama ministan raya tattalin arziki na tarayya, sannan daga 1960 zuwa 1962 aka sake nada shi mukamin ministan fansho na tarayya. Ya ci gaba da zama ministan harkokin cikin gida na tarayya daga 1962 zuwa 1965, kuma kafin juyin mulkin farko na soja a watan Janairun 1966 ya kasance ministan ayyuka na tarayya.

Shagari ya samu karbuwa sosai saboda saukin kai, tawali’u, da jajircewarsa wajen yi wa gwamnati hidima. Wa’adinsa na shugaban kasa ya kasance da kokarin inganta hadin kan kasa da ci gaban tattalin arziki, duk da cewa kasar na fuskantar kalubalen tattalin arziki da siyasa.

 

Ernest Shonekan

Cif Ernest Shonekan ya rasu ne a ranar 11 ga watan Junairu, 2022, yana da shekaru 85, sakamakon kamuwa da cutar huhu a wani asibitin Legas. Ana tunawa da shi a matsayinsa na shugaban rikon kwarya na Nijeriya a shekarar 1993, gwamnatin rikon kwarya da ta shafe watanni kadan kafin a hambarar da shi a juyin mulkin da Janar Sani Abacha ya yi a fadarsa.

Kafin shiga fagen siyasa Shonekan ya yi fice a harkar kasuwanci. Ya kasance shugaba kuma babban jami’in gudanarwa na Kamfanin United African Company of Nigeria (UACN), babban kamfani na Nijeriya kuma magajin kamfanin The Niger.

A karkashin jagorancinsa, UACN na daya daga cikin manyan kamfanoni da ke karkashin ikon Afirka a yankin kudu da hamadar sahara, masu bukatu daban-daban a masana’antu, noma, da kuma ayyuka. Kwarewar Shonekan a matsayin lauya da dan kasuwa ya samu karbuwa sosai, kuma ana ganin nadinsa a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya a matsayin wani yunkuri na daidaita Nijeriya a lokacin da ake cikin rashin tabbas na siyasa. Duk da dan gajeren wa’adinsa, shugabancinsa ya nuna wani muhimmin lokaci na komawar Nijeriya mulkin farar hula.

 

Muhammadu Buhari

Janar Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a birnin Landan yana da shekaru 82. An haife shi a ranar 17 ga Disamba, 1942, a garin Daura na Jihar Katsina, Buhari ya yi dogon zango da fice a harkokin soja da na farar hula. Ya taba zama Gwamnan Soja na tsohuwar Jihohin Borno da Arewa ta Tsakiya tsakanin 1975 zuwa 1976, inda ya nuna kwarewar tafiyar da mulki tun farko da za ta yi tafiyarsa ta siyasa a baya.

A matsayinsa na Janar din soja mai ritaya, Buhari ya kuma rike mukamin kwamishinan albarkatun man fetur na tarayya a lokacin mulkin soja na tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, daga 1976 zuwa 1979, yana sa ido a kan muhimmancin mai a Nijeriya. Da hawansa ya kai kololuwa a cikin watan Disambar 1983 a lokacin da ya jagoranci juyin mulkin da ya yi nasara a juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin farar hula ta Shugaba Shehu Shagari.

Daga nan ne Buhari ya yi mulki a matsayin shugaban kasa har zuwa watan Agustan 1985, inda Manjo Janar Tunde Idiagbon ya zama shugaban ma’aikatan fadarsa.

Gwamnatinsa dai ta shahara da tsauraran matakan yaki da cin hanci da rashawa da kuma kokarin ladabtar da ma’aikatan gwamnati, duk da cewa ta fuskanci suka kan take hakkin dan’Adam da kalubalen tattalin arziki.

A karshe dai an hambarar da gwamnatin Buhari a wani juyin mulkin da sojoji suka yi karkashin jagorancin Janar Ibrahim Babangida.

Bayan shafe shekaru a kan mulki, Buhari ya sake fitowa a matsayin shugaban dimokuradiyya, inda ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2015 a karkashin jam’iyyar APC.

An sake zabarsa a shekara ta 2019, wanda ke nuna sauyin tarihi a matsayin tsohon shugaban mulkin soja na farko da aka zabe shi sau biyu a matsayin farar hula.

Shugabancinsa ya mayar da hankali sosai kan yaki da cin hanci da rashawa, kalubalen tsaro kamar tada kayar baya da ‘yan fashi, da sake fasalin tattalin arziki. Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2023, inda ya mika mulki cikin lumana ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A tsawon rayuwarsa, Buhari ya kasance wani jigo a fagen siyasar Nijeriya da wasu ke mutuntawa saboda horo da azamarsa, wasu kuma na sukar yadda ake ganin mulkinsa na kama karya. Mutuwarsa ta kawo karshen zamanin da ya shafi tarihin soja da dimokuradiyyar Nijeriya.

Rasuwar wadannan tsofaffin shugabannin kasar ya kawo karshen cece-kuce na wadanda suka tsunduma cikin harkar siyasar Nijeriya. Tun daga mulkin soja zuwa sauye-sauyen dimokuradiyya, abubuwan da suka gada, suna ci gaba da tsara tunanin al’umma baki daya. Yayin da kasar ke ci gaba, labaransu sun zama abin tunatarwa kan dorewar tasirin shugabanci, hidima, da kuma ci gaba da tafiyar da mulkin Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Xi Jinping Ya Karbi Takardun Nadi Daga Sabbin Jakadun Kasashen Waje
  • Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
  • Fahimtar Sabon Tunani: Mene Ne Birnin Zamani Na Al’umma
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
  • Tursasawa Kasashen Afirka Karbar Bakin Haure Daga Amerika Kuskure Ne
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas
  • Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran