A cewar ministan, shi da sauran abokan aikin sa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin ƙaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a Jihar Katsina.

 

Cibiyoyin da aka ƙaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sababbin cibiyoyin maganin ciwon daji guda shida a manyan Asibitocin Koyarwa na Tarayya a ƙasar nan.

 

Wannan cigaba wani muhimmin mataki ne wajen rage wahalar da marasa lafiya ke fuskanta wajen samun ingantacciyar kulawa, da kuma hana fita ƙasashen waje don neman magani.

 

Gwamnatin ta tabbatar da cewa sauran cibiyoyin da suka rage za su kammala nan ba da jimawa ba domin cika alƙawarin samar da ingantaccen tsarin lafiya ga kowa da kowa a Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza

Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin.

Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.” Motocin suna dauke da kayan abinci, ruwa da magani a cikin kasashen Jordan da Masar.

 A wani bayani da ofishin gwamnatin Gaza ya fitar a yau Alhamis, a cikin yankin Gaza duk wani abinci, ruwa da magani duk sun kare, don haka a halin yankin yankin yana da bukatuwa da buhunan filawa 500,000 a kowane mako.

 An shiga kwanaki 145 da HKI ta rufe dukkanin mashigar Gaza, da hana shigar da madarar jarirai da dukkanin kayan agaji.

Bugu da kari ofishin gwamnatin Gaza din ya kuma kara da cewa; Da akwai wasu kafofi da suke watsa jita-jita da karairayi akan shigar da kayan abinci zuwa cikin yankin na Gaza, yana mai cewa babu kamshin gaskiya a ciki.

Haka nan kuma ya yi kira ga mutanen Gaza da kar su yarda da wadannan irin karairayin, wacce manufarta rufe hakikanin laifukan da ‘yan sahayoniya suke aikatawa.

Har ila yau, ofishin na gwamnatin Gaza ya bukaci ganin dukkanin kasashen duniya ba tare da togiya ba, da su yunkura domin karya killace Gaza da aka yi, da kuma bude kan iyakoki saboda a shigar da madarar da kananan yara za su sha, da kuma abincin da mutane fiye da miliyan 2.4 za su ci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 3.5 Wajen Gina Shaguna A Farm Centre
  • Jihohin Da Ke Shirin Rage Kudin Wutar Lantarki Su Shirya Biyan Tallafi – Ministan Wuta
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Jaddada Aniyar Iran Ta Ci Gaba Da Inganta Sinadarin Uranium
  • ‘Yan Nijeriya Miliyan 40 Ke Fuskantar Barazanar Kwararowar Hamada – Ministan Muhalli
  • Iran: Iran Tana Cikin Kasashe Biyar Na Duniya Da Suka Ci Gaba Wajen Kiwon Dabbobi
  • Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza
  • Ministan Lafiya Na Kamaru: Hadin-Gwiwa Ta Fuskar Kiwon Lafiya Ta Shaida Zumunci Mai Karfi Tsakanin Kamaru Da Sin
  • Iran Tace Tawagar Kwararru Daga Hukumar IAEA Zata Ziyarci Kasar Nan Ba Da Dadewa Ba
  •  Iraki Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Akan Dakarun Sa Kai Na” Hashdus-sha’abi”