Ina Karanta Rantsuwar Da Na Yi A Kullum Don Tuna Nauyin Da Ke Kaina-Gwamna Namadi
Published: 25th, July 2025 GMT
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa yana yawan karanta rantsuwar kama aiki da ya yi domin tunatar da kansa nauyin da ya dauka na yi wa al’umma hidima bisa gaskiya da amana.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba bayan nadin sabon shugaban karamar hukumar Gumel.
A wajen bikin da aka gudanar a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Dutse, Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa rayuwa na da kurarran lokaci, don haka ya kamata shugabanni su kasance masu tsoron Allah da kuma sanin nauyin da ke kansu.
“Rayuwa ba ta da tabbas, hakazalika shugabanci ba wasa ba ne”. In ji shi.
Ya bukaci masu rike da madafun iko da su kasance masu kula da al’amuransu cikin tsoron Allah da sanin cewa akwai ranar hisabi da mutuwa.
Da yake jawabi ga sabon shugaban karamar hukumar, Gwamnan ya ce: “Rantsuwar da ka dauka ita ce mu ma muka dauka. Na ajiye tamu a kan teburi a ofishina, kuma kullum ina karanta ta. Ina ba ka shawarar kai ma ka rika karanta taka kafin ka fara aiki a kullum.”
Ya ja hankalin sabon shugaban da kada ya bari son zuciya ya shige masa gaba wajen gudanar da ayyukansa, yana mai cewa son kai na daga cikin manyan matsalolin da ke gurgunta mulki mai nagarta.
Ya bukaci sabon shugaban da ya yi aiki da kowa, ya rika tuntubar masu ruwa da tsaki, tare da sanya mutanen da ya ke wakilta gaba a kowanne lokaci.
Gwamnan ya kammala da cewa shugabanci yana bukatar hakuri, kwarewa, da tsoron Allah, yana mai cewa“babu wanda aka haifa da basirar shugabanci, amma da kaskantar da kai da tsoron Allah, za ka yi nasara”
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙungiyar Rays Heaven ta Ƙarfafa Wayar da Kai kan Lafiyar Kwakwalwa a Kaduna
Daga Abdullahi Shettima.
Ƙungiyar taimako mai zaman kanta mai suna Rays Heaven for Special Needs Children and Adults ta gudanar da taron wayar da kai a Kaduna domin ƙarfafa fahimtar muhimmancin kula da lafiyar kwakwalwa da kuma magance matsalolin tattalin arziki da ke shafar rukunin jama’a masu rauni.
Shugaban shirye-shiryen ƙungiyar, Sadiq Abdilatif, ya bayyana cewa wannan shiri mai taken Youth Resilience Project ana aiwatar da shi ne da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (European Union) tare da Global Youth Mobilization Fund.
Ya ce manufar shirin ita ce wayar da kai ga makarantun sakandare, al’ummomi, da sansanonin ’yan gudun hijira kan mahimmancin lafiyar kwakwalwa, tare da ƙarfafa matasa su koyi magana idan suna fuskantar damuwa ko matsaloli, da kuma koyar da malamai da shugabannin al’umma hanyoyin taimaka musu.
Mr. Abdilatif ya bayyana cewa matasa da mutane masu buƙata ta musamman, ciki har da ’yan gudun hijira, na fama da ƙalubalen tunani da na tattalin arziki da ke rage musu ƙarfi wajen gudanar da rayuwa. Ya ce wannan shiri yana nufin gina ƙarfin gwiwa da samar da wakilai a cikin al’umma waɗanda za su ci gaba da yada wannan saƙo a yankunansu.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar na da shirin haɗa shugabannin gargajiya da na addini domin tabbatar da ci gaba da wayar da kai a matakin ƙasa, yana mai cewa batun lafiyar kwakwalwa abin ne da ya shafi kowa.
Ɗaya daga cikin mahalarta shirin, Salma Hussaini, wadda ba ta da gani, ta yaba da yadda ƙungiyar ta haɗa masu buƙata ta musamman a cikin shirin. Ta ce ta amfana sosai wajen fahimtar yadda ƙarfin tunani da dogaro da kai ke taimakawa mutum ya shawo kan ƙalubalen da yake fuskanta duk da rashin lafiyar jiki.