Ya ce tituna a Arewa sun lalace kuma gwamnati tana nuna rashin kulawa ga yankin. “Jiya da jirgi zan biyo na taho, amma aka ɗage jirgi daga ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare, sai na taho ta mota. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano abin takaici ne. Wannan aikin titi tun lokacin farkon hawa gwamnatin APC ake yinsa.

Kwankwaso ya kara da cewa ana gudanar da manyan ayyuka a Kudu cikin hanzari, amma an bar ayyuka masu mahimmanci a Arewa babu kulawa.

“Muna jin ana gina titi daga Kudu zuwa Gabas. Muna maraba da ci gaba a ko’ina a Nijeriya. Amma gwamnati tana ɗaukar duk arzikin ƙasa ta zuba a ɓangare ɗaya kaɗai, ba ta yin aiki da ra’ayin ‘yan ƙasa gaba ɗaya,” cewarKwankwaso.

Ya roƙi gwamnatin Tinubu da ta sake duba tsarin rabon arziki tare da tabbatar da yin adalci a dukkan yankuna.

“Lokaci ya yi da gwamnati za ta sauya, ta tabbatar wa da ’yan Nijeriya cewa gwamnati ce ta ƙasa gaba ɗaya, ba ta wani ɓangare kawai ba,” in ji Kwankwaso.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Arewa Ɓangarenci Kwankwaso Nijeriya Nuna wariya

এছাড়াও পড়ুন:

Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 

Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.

 

Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.

 

Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.

 

Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.

 

Sai dai kasa da wata guda da kulla yarjejeniyar, an tattaro cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a Zamfara inda suka yi awon gaba da masallata da dama.

 

Wata majiya ta cikin garin, ta shaida cewa, harin ya afku ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa masallacin, suka kewaye shi, sannan suka tattara masallatan zuwa daji.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta