Iran: Iran Tana Cikin Kasashe Biyar Na Duniya Da Suka Ci Gaba Wajen Kiwon Dabbobi
Published: 24th, July 2025 GMT
Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen dabbobi.
Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da nono ta hanyar kyautata da kula da lafiyarsu, domin rage dogaro da waje samar da nama da kuma nono.
Haka nan kuma ministan na noma ya kara da cewa; Kara yawan dabbobin da ake samarwa a cikin gida,wata lalura ce ta tattalin arziki, da kuma kishin kasa.
Ministan Noma na Iran ya kuma kara da cewa, ma’aikatar tasu tana kokarin ganin mayar da Iran zama cibiyar samar da abinci mafi girma a cikin wannan yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Binciken Jin Raayoyi Na CGTN: Duniya Ta Saba Da “Kauracewar” Amurka
Ficewar Amurka daga yarjejeniyoyin kasa da kasa da hukumomin duniya ba sabon labari ba ne, don haka mene ne abun mamaki idan ta bar UNESCO a karo na uku? Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar ya nuna cewa kashi 84.2 cikin dari na wadanda suka bayyana rayoyinsu ba su yi mamakin wannan matakin ba, lamarin da ke nuni da cewa, kasashen duniya sun saba da halayyar “kauracewar” Amurka. Wannan mataki na “Amurka ta zamanto farko” yana kara ingiza bukatar tsarin damawa da mabambantan bangarori na hakika cikin hanzari.
Hujjar gwamnatin Amurka a wannan karon ta kasance a sarari, watau ta zargi UNESCO da ci gaba da zurfafa tabbatar da “mabambantan tsarin zamantakewa da al’adu” wadanda suka ci karo da manufarta ta “Amurka ta zamanto farko”. A cewar sakamakon binciken, kashi 93.5 na masu bayyana raayoyi sun soki Amurka bisa mayar da cibiyoyin kasa da kasa a matsayin kayan aikin cimma muradunta na siyasa.
Binciken jin ra’ayoyin ya nuna cewa kashi 90.7 cikin dari na wadanda suka bayyana raayoyinsu suna kallon ficewar baya-bayan nan a matsayin karin tabbaci na yadda Amurka ke nuna son zuciya saboda Isra’ila, yayin da kashi 91.1 cikin dari na jamaar da suka bayyana raayoyin nasu suka nuna cewa, tsarin mu’amalarta da hukumomin kasa da kasa bai zamo mai alfanu ga wata babbar kasa ba, ko kuma biyan bukatun kasashen duniya.
Wanda aka gudanar a kafofin CGTN na harsunan Ingilishi, da Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci, binciken ya tattaro raayoyin jamaa 9,097 cikin sa’o’i 24. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp