Leadership News Hausa:
2025-12-13@01:44:08 GMT

Kawunan Shugabannin Arewa Sun Rabu Kan Siyasar 2027

Published: 26th, April 2025 GMT

Kawunan Shugabannin Arewa Sun Rabu Kan Siyasar 2027

Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

 

Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba.

 

Da yake magana ta wayar tarho a ranar Lahadi, sakataren yada labarai na ACF na kasa, Farfesa T.

A. Muhammad Baba, wanda aka nemi ya yi tsokaci kan kalaman Baba-Ahmed, ya ce a matsayinsa na dattijo, Baba-Ahmed yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa.

 

Mai magana da yawun ACF, duk da haka, kungiyar za ta bincika dukkan batutuwan tare da gabatar da su ga masu jefa kuri’a don su iya yin zabi mai kyau a 2027.

 

“Dakta Baba-Ahmed yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa. Bai dade da ya bar cikin gwamnati ba, kuma duk abin da ya ce hakkinsa ne. Kun san muna gab da zabukan 2027, kuma yawancin irin wadannan ra’ayoyin mutane da kungiyoyi za su bayyana a yayin da zabuka ke gabatowa. Muna sa ran ganin karin irin wannan sharhi. Ko yake, ACF ba kungiya ce ta siyasa ba. Ba ma nuna bangaranci.

 

“Yayin da zabe ke gabatowa, za mu iya nazarin batutuwa ne kawai mu gabatar da su ga masu jefa kuri’a don su yanke shawarar wanda za su zaba. Ba za mu bayyana goyon baya ga duk wani dan takarar jam’iyyar siyasa da zai tsaya takara a zaben shugaban kasa a 2027 ba. Za mu ci gaba da kasancewa a matsayin kungiyar kare muradun al’ummar Arewa,” in ji ACF.

 

A halin da ake ciki, wata kungiya mai suna ‘Arewa Think Tank’ (ATT), ta nuna goyon baya ga matsayin Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule cewa ya kamata Arewa ta yi aiki don sake zaben Bola Tinubu a 2027.

 

A kwanan nan ne Gwamna Sule ya bayyana cewa Arewa na bukatar hada kai don aiwatar da yunkurin Shugaba Tinubu ba.

 

A kan kashe-kashen da aka yi kwanan nan a jihohin Filato da Benuwai, Arewa Think Tank ta yi zargin cewa makiyan ‘yan siyasa suna yin duk mai yiwuwa, ciki har da shigar da kasashen waje, don kawo cikas ga gudanar da babban zabben 2027.

 

A cikin wata sanarwa da shugaban ATT, Muhammad Alhaji Yakubu ya fitar, ya ce kungiyar ta sha alwashin goyon bayan yin tazarcen Shugaba Tinubu, domin ya ci gaba da ayyukan da ya faro.

 

“Mun san cewa goyon bayan wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu zai cika alkawarin da ya yi wa yankin Arewa tun gabanin babban zaben 2023.

 

“Mun amince kuma mun goyi bayan Gwamna Sule saboda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ta tsakiya, kuma mun san cewa ba a san Arewa da yin watsi da alkawuran da ta dauka ba.”

 

ATT ta bukaci shugabannin Arewa da su nesanta kansu daga wasu ‘yan siyasa da ke da niyyar rikitar da siyasar Nijeriya saboda sun kasa cimma burinsu.

 

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rufe kan iyakokin kasar nan tare da hana bakin haure shigowa Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria

 

 

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Yadda Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samar Da Karin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa December 11, 2025 Daga Birnin Sin Kamfanonin Sin Sun Kera Tare Da Sayar Da Motoci Sama Da Miliyan 31 Tsakanin Janairu Zuwa Nuwamban Bana December 11, 2025 Daga Birnin Sin Bankin Duniya Ya Daga Hasashen Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na 2025 Da Maki Kaso 0.4 December 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe
  • Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago
  • Kungiyar NLC A Najeriya Ta Shirya Zanga-Zanga Kan Matsalar Rashin Tsaro A Fadin Kasa
  • Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda
  • Taron Abuja kan Tattaunawakan Tattalin Arziki Kasa- “Akwai yiyuwar tattalin arzikin kasa zai murmure a shekarar 2026”
  • Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
  • Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria
  • ‘Yan Siyasa Ne Ke Zagon Ƙasa Ga Ci Gaban Nijeriya — Sarki Sanusi II
  • Shugabannin Sin Sun Yi Taron Koli Na Tattauna Aikin Raya Tattalin Arziki Don Tsara Abubuwan Da Za A Aiwatar A 2026