HausaTv:
2025-07-26@04:23:28 GMT

Iran da Bangladesh sun bukaci taron gaggawa na OIC kan kisan kiyashi a Gaza

Published: 25th, July 2025 GMT

Kasashen Iran da Bangaladesh sun yi kakkausar suka ga cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, tare da yin kira ga al’ummar musulmi da su dauki matakin gaggawa na dakatar da yakin kisan kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi wa al’ummar Palasdinu.

A wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Bangladesh Md.

Touhid Hossain sun yi musayar ra’ayi kan halin da ake ciki a yankin.

Araghchi ya yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila take tabkawa,  musamman manufofinta  na hana Falasdinawa abinci da Ruwan sha. Ya kuma jaddada muhimmancin kiran taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kuma samar da dukkanin hanyoyin da za a bi don dakile kisan kare dangi da kuma tinkarar laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila.

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma yi gargadi game da yunkurin Tel Aviv na mamaye yankin yammacin kogin Jordan, yana mai bayyana hakan a matsayin wani babban shirin yahudawan sahyoniya na kawar da batun Palastinu.

Ya kuma yi kira ga kasashen musulmi da su dauki kwararan matakai na hadin gwiwa domin dakile kisan kiyashin da kuma kai agajin jin kai ga al’ummar Palasdinu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki

Yan majalisar dokokin kasar Iran sun bukaci majalisar dokokin kasar Iraki su kori sojojin Amurka daga kasar ta Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran yana cewa, yan majalisar dokokin kasar Iran sun bayyana haka ne a lokacin ganawasu da wani dan majalisar dokokin kasar  Iraki mai wakiltan lardin Karbalar Imam Hussain (a) a majalisar dokokin kasar.

Labarin ya nakalto wakilin lardin Karbala a majalisar dokokin kasar Iraki yana cewa kasashen Iran da Iraki da gwamnatin kasar Iraki sun gamu a wannan ra’ayin kuma nan gaba abinda za’a yi Kenan. Yace dole ne sojojin Amurka su fice daga kasar Iraki, su kuma fice daga dukkan kasasjen larabawa a yankin. Ya ce da haka ne kasashen yankin zasu tabbatar da tsaron yankinsu.

Ebrahim Rezae dan majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa, kasar Amurka baa bin Amincewa ne, kuma shirin HKI na fadada mamayar karin yankunan kasashen larabawa na tafiya ne tare da umurnin Amurka kai tsaye.

A ranar 3 ga watan Jenerun Shekara ta 2020 ne shugaban Donal Trump ya bada umurnin kashe babban kwamandan rundunar Qudus ta Iran Janar Shahid Qasim Sulaimani a lokacinda ya shigo kasar Iraki daga Siriya tare da gayyatar gwamnatin kasar ta Iraki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Jaddada Wajabcin Daukan Matakin Kawo Karshen Dakatar Da Laifukan Kisan Kare Dangi A Gaza
  • Ayatullahi Makarem Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kai Da Suka Bayar Lokacin Yakin Kwanaki 12
  • Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Tattaunawa kan Masifar Zirin Gaza Na Falasdinu
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  • Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!
  • Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Na Isra’ila Da Makami Mai Linzami Nau’in Flasdinu
  • Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
  • Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran