Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Tattaunawa kan Masifar Zirin Gaza Na Falasdinu
Published: 24th, July 2025 GMT
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza.
Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yankin Gabas, Mohamed Khaled Khari, ya tabbatar da cewa an kashe Falasdinawa kusan 300 a kusa da wuraren raba kayan agaji tun bayan jawabinsa na karshe a watan jiya.
“Mummunan halin da ake ciki a Gaza yana kara tabarbarewa tare da karuwar hasarar rayuka. Dole ne a daina yakin Gaza kuma a sako mutanen da aka yi garkuwa da su. Ayyukan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Deir al-Balah ya haifar da karuwar ‘yan gudun hijira.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran da Bangladesh sun bukaci taron gaggawa na OIC kan kisan kiyashi a Gaza
Kasashen Iran da Bangaladesh sun yi kakkausar suka ga cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, tare da yin kira ga al’ummar musulmi da su dauki matakin gaggawa na dakatar da yakin kisan kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi wa al’ummar Palasdinu.
A wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Bangladesh Md. Touhid Hossain sun yi musayar ra’ayi kan halin da ake ciki a yankin.
Araghchi ya yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila take tabkawa, musamman manufofinta na hana Falasdinawa abinci da Ruwan sha. Ya kuma jaddada muhimmancin kiran taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kuma samar da dukkanin hanyoyin da za a bi don dakile kisan kare dangi da kuma tinkarar laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma yi gargadi game da yunkurin Tel Aviv na mamaye yankin yammacin kogin Jordan, yana mai bayyana hakan a matsayin wani babban shirin yahudawan sahyoniya na kawar da batun Palastinu.
Ya kuma yi kira ga kasashen musulmi da su dauki kwararan matakai na hadin gwiwa domin dakile kisan kiyashin da kuma kai agajin jin kai ga al’ummar Palasdinu.