Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
Published: 24th, July 2025 GMT
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza
Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF a Falasdinu, ya tabbatar da cewa: Abin da ke faruwa a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar wasu ma’aikatan jin kai da dama da suka yi balaguro zuwa yankunan da ake fama da rikici, da bala’o’i, da wuraren yaki a duniya, kuma dukkansu, ba tare da togiya ba, sun amince cewa, ba su taba ganin wani yanayi mai kama da abin da ke faruwa a Gaza ba.
Abu Khalaf ya yi nuni da cewa: Mutanen yankin Zirin Gaza sun fara fama da yunwa, sannan kuma kishirwa, gami da fuskantar kisa, yayin da aka jibge kayan agajin jin kai a kan iyakar da ke da tazarar kilomita goma kacal. Motar bas guda na iya daukar sa’a guda-ko kuma akalla sa’a daya da rabi kafin ta isa tsakiyar zirin Gaza da agaji, amma sojojin mamayar Isra’ila ba za su kyale ta.
Ya bayyana cewa, kasashen duniya suna nuna halin ko-in-kula, tare da nuna rashin damuwa da daukan abin da muhimmanci daga Larabawa a hukumance da kuma juya baya daga al’ummar Larabawan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Jaddada Wajabcin Daukan Matakin Kawo Karshen Dakatar Da Laifukan Kisan Kare Dangi A Gaza
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin dakatar da kisan kare dangi a Gaza
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Aref ya jaddada cewa: Dole ne a kawo karshen kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankin Zirin Gaza cikin gaggawa ta hanyar daukar matakai na zahiri da kuma dauri daga kasashen duniya.
Aref ya rubuta a shafinsa na X a jiya Alhamis cewa: “Mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba saboda yunwa sakamakon hana isar da abinci ga al’ummar Gaza da aka zalunta ya kasance tare da yin shiru na kunya daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.”
Ya kara da cewa: “Dole ne a kawo karshen wannan kisan kiyashi da ake yi a fili ta hanyar daukar matakai na zahiri da kasashen duniya zasu dauka, sannan kuma a hukunta wadanda suka aikata wannan laifin na cin zarafin bil’adama.”
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Zirin Gaza ta sanar a cikin wata sanarwa cewa: A cikin sa’o’i 24 da suka gabata an kashe mutane 89 a zirin Gaza, yayin da wasu 453 suka jikkata.