‘Yan Tawayen Sudan Ta Kungiyar Rapid Support Forces Sun Kashe Mutane 27 A Yammacin Jihar Kordofan Ta Kasar Sudan
Published: 25th, July 2025 GMT
Mutane akalla 27 ne aka kashe a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai a yammacin Kordofan na kasar Sudan
Kafofin yada labaran kasar Sudan sun rawaito cewa: Mutane 27 ne suka mutu kana wasu 43 suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai kan wasu kauyukan arewacin garin Nahud na jihar Kordofan ta yamma.
Kungiyar likitocin Sudan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jaridar Sudan Tribune ta buga, inda ta bukaci daukar matakin kasa da kasa na dakatar da abin da ta bayyana a matsayin “cin zarafin fararen hula da bude hanyoyin jin kai don ceto wadanda aka tilastawa gudun hijira daga yankunansu.”
A cewar jaridar, dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces ne ke rike da mafi yawan yammacin Kordofan, ciki har da babban birnin jihar, Al-Fula, yayin da sojoji ke iko da Babanusa da wasu gidajen mai a Heglig.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Jarida Da Suka yi Shahada A Gaza Sun Kai 232, Yayin Da Wadanda Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Yunwa Suka Kai 122
‘Yan jarida akalla 232 suka yi shahada sannan wasu 122 sun rasa rayukansu sabaoda masifar yunwa a yankin Zirin Gaza!
Yakin kisan kare dangi da ake yi a zirin Gaza yana ci gaba da lakume rayukan Falasdinawa da dama a kowace rana, manya da kanana…ta hanyar jefa bama-bamai, kisa, killace yankin da kakaba masifar yunwa.
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu daruruwa, ciki har da masu neman agaji, sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar al-Rimal da gidaje da sansanonin ‘yan gudun hijira a yankunan al-Amal, al-Tuffah, da al-Nasr, dake gabashi, arewacin Gaza.
Hakazalika an sha kai hare-hare ta sama a yankunan al-Balad da al-Amal da ke Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza, da kuma harin bama-bamai da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila.