Aminiya:
2025-07-23@22:45:23 GMT

Bom ɗin Boko Haram ya kashe fasinjoji 9 a tashar mota a Borno

Published: 2nd, June 2025 GMT

Mutane tara sun mutu wasu da dama sun jikkata sakamakon tashin wani abu mai fashewa da ’yan Boko Haram suka dasa a ƙauyen Mairari da ke Ƙaramar Hukumar Guzamala ta Jihar Borno.

Lamarin ya faru a wata tashar mota a kauyen, wanda ke da nisan kilomita 18 daga Karamar Hukumar Monguno da kuma kilomita 119 daga Maiduguri.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkarim Lawan, mai wakiltar yankin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin “rashin imani.”

Abdulkarim Lawal ya bayyana cewa waɗanda lamarin ya shafa mazauna yankin ne masu juriya da ke komawa gonakinsu a Mairari.

NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa Layya da hukunce-hukuncenta a Musulunci

Kafin yanzu, sau biyu ana sake tsugunar da mutanen yankin bayan sun yi gudun hijira, amma hare-haren Boko Haram na sake tilasta musu yin ƙaura.

Lawan ya yi kira ga sojoji da su ƙaddamar da ayyuka masu zafi domin ƙwato ɗauƙacin Ƙaramar Hukumar Guzamala, ciki har da Gudumbali da Mairari, waɗanda ya ce suna ƙarƙashin ikon ’yan ta’adda.

Shugaban majalisar ya ce, “Abin takaici ne yadda mutane tara daga cikin al’ummata masu juriya suka mutu sakamakon fashewar bom da aka dasa yayin da suke jiran shiga motocin haya a wata tashar mota a kauyen Mairari.”

Ya addu’ar samu rahama ga mamatan da kuma samun lafiya ga wadanda suka jikkata.

Ya yaba da ƙoƙarin sabon Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar, amma ya sake jaddada buƙatar gaggawa ta dawo da mulkin farar hula a yankunan da abin ya shafa.

A sauya wa Barikin Giwa wuri — Kungiyar Bale Galtimari

A wani labarin mai nasaba da hakan, Ƙungiyar Tuntuɓa ta Bale Galtimari ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kawar da barikin sojoji na Giwa daga inda yake a Maiduguri.

Dakta Zanna Boguma, shugaban kungiyar, ya bayyana yadda Boko Haram ke kai hare-hare akai-akai ga barikin, lamarin da ke jefa rayuwar mazauna yankin fiye da miliyan daya cikin hadari a yankunan farar hula kamar Galtimari, Fori, da 122.

Ya lura cewa barikin, wanda ake kyautata zaton yana tsare da ’yan ta’adda, an kai masa hari akai-akai domin sakin su, a 2014, 2015 (sau uku), da 2019.

Ƙungiyar ta jaddada cewa bai kamata a gina manyan sansanonin sojoji a cikin al’ummomin farar hula ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Galtimari

এছাড়াও পড়ুন:

Dalilin da muka gaza biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi — Gwamnatin Borno

Gwamnatin Borno ta bayyana yawan ma’aikata a matsayin dalilin da ya sanya ƙananan hukumomin jihar ba za su iya biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata na Naira dubu 70,000 ba.

Gwamnatin ta ce ta umarci shugabannin ƙananan hukumomin jihar su samar da tsari mai ɗorewa domin ƙaddamar da fara aikin mafi ƙarancin albashin.

WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi

Babban sakataren ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masana’antu, Modu Alhaji cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce yawan ma’aikatan ne ya haifar da jinkiri wajen fara biyan mafi ƙarancin albashin.

Modu ya yi bayanin cewa a wasu lokutan gwamnatin tarayya na turo ƙasa da Naira miliyan 700 zuwa asusun ƙananan hukumomin domin biyan albashin, a wani yanayi da ake buƙatar Naira miliyan 778 domin biyan ma’aikata albashi.

Gwamnatin ta yi nuni da cewa, Jihar Kano da ke da ƙananan hukumomi 44 na da ma’aikata dubu 30,000 ne kawai, amma Borno da ke da 27 na da ma’aikatan ƙananan hukumomi da yawansu ya kai dubu 90,000.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid A Borno
  • Dalilin da muka gaza biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi — Gwamnatin Borno
  •  Fiye Da  Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da HKi Ta Jefa Mutanen Gaza A Ciki
  • A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
  • Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!
  • Eritrea ta gargadi Habasha game da yunkurin kafa tashar jiragen ruwa a cikin yankinta
  • Gwamna Radda Da Makarrabansa Na Samun Kulawa A Asibiti Bayan Hatsarin Mota A Hanyar Daura
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin
  • Jaridar Washington Post Ta Ce; Yeman Ta Gurguta Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Isra’ila