Majalisar Dokokin Katsina Ta Ayyana Gwamna Radda A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A 2027
Published: 1st, June 2025 GMT
Hon. Nasiru ya kara da cewa Gwamna Radda ya yi kokari wajen yaki da matsalolin tsaro wanda suka addabi Jihar Katsina, inda ya bayyana cewa ana samun sauki sosai a wannan bangare.
Ya ce gwamnati ta gyara makarantu da asibitoci a fadin Jihar Katsina, inda aka maida su na zamani tare da daukar ma’aikatan lafiya da kuma malaman makaranta da yawansu ya kai 7,000, wanda ya ce ko haka aka tsaye suna da hujja da dalilin mara masa baya.
Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne, ‘yan majalisun tarayya guda 15 dukkansu na jam’iyyar APC suka ayyana Gwamna Radda a matsayin wanda za su goya baya a zaben 2027.
Sai dai kuma ana dora ayar tambaya kan wadannan ‘yan majalisu da cewa sun yi riga Malam Masallaci, domin kafin su yanke irin wannan hukunci ya kamata su tuntubi wadanda suke wakilta domin gudun tutsu ranar zabe.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne, Gwamna Radda zai maida biki, ma’ana dai shi ma ya amince kowane dan majalisa ya dawo kujerarsa ba tare da hammaya ba? Lokaci alkali!
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gwamna Radda
এছাড়াও পড়ুন:
Rayuwata Na Cikin Hatsari, A Dawo Min Da Jami’an Tsarona – Natasha
“Saboda barazanar tsaro da ke tattare da al’amuran siyasa, da kuma buƙatar kare lafiyata yayin gudanar da aiki, ina roƙon a dawo min da jami’an tsarona,” in ji ta.
Ta kuma haɗa da kwafin hukuncin kotun, inda ta jaddada marnin dawo da ita bakin aiki.
Sai dai komawarta majalisa ya haifar da ce-ce-ku-ce, domin Majalisar Dattawa ta ce hukuncin kotun da Sanata Natasha ke dogaro da shi ba dole ba ne a aiwatar da shi, domin ba umarni ba ne kai-tsaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp