Zulum Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Mata ‘Yan Asalin Jihar Da Suka Samu Maki 250 A JAMB
Published: 1st, June 2025 GMT
Gwaman ya umarci mai rikon mukamin Shugaban ma’aikata, Hukumar bada tallafin karatu ta Jihar, ma’aikatar ilimi,da kuma kungiyar APWEN reshen Maiduguri cewar wadanda suka cika sharuddan da ake bukata ya dace a basu tallafin na karatu.
Lokacin taron ya taya Shugabnnin kungiyar amsu barin gado da kuma wadanda za su gaje su kan jajircewar da suka nuna wajen daukakalamarin da ya shafi kwararru ta bangaren Injiniya.
Da take gabatar da kasida mai taken, “Muhimmancin daukar nauyin da jawo hankalin’ ya’ya mata su yi karatun Injiniya da daukar abin a matsayin aiki a Nijeriya, ”Uwargidan gwamnan Borno,Dakta Habiba Babagana Zulum, ta lura da cewar daukar nauti wani lamari ne na yadda ake bunkasa ci gaban kwararru,inda ta yi nunu da cewa mata a Nijeriya sun samar da kashi 14 ne cikin 100 na ma’aikatan da suke da alaka da STEM, tace barin fiye da kashi 50 na yawan mutanen da basu da alaka da STEM wajen gina kasa wani abinda bai dace bane.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Magudnar Ruwa Ta Yi Ajalin Rayuka Hudu A Zangon Kaya, Kano
Mazauna unguwar Zangon Kaya da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano sun shiga cikin makoki sakamakon nutsewar da wasu matasa hudu suka yi a hanyar ruwa da baraguzan gine-gine suka tushe.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
A cewarsa, lamarin ya faru ne bayan wadanda lamarin ya rutsa da su suka shiga mashigar ruwa da suka taru sakamakon toshewar hanyar jirgin da ake yi.
Ya kara da cewa, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, da farko biyu daga cikin wadanda abin ya shafa sun shiga cikin ruwan da nufin yin iyo amma sun makale. A kokarin ceto su, mutum na uku ya shiga, shi ma ya makale. Abin baƙin ciki, mutum na huɗu, yana ƙoƙari ya ceci sauran, ya fuskanci irin wannan matsalar.
Saminu ya yi nuni da cewa, kafin isowar hukumar kashe gobara mazauna yankin sun yi nasarar ceto biyu daga cikin wadanda abin ya shafa. Yayinda “Sauran biyun, tawagar ceto ta fito da
Wadanda abin ya shafa sun hada da Nasirudden Tasi’u dan shekara 25 da Basir Sani mai shekaru 28 da Yakubu Muhd dan shekara 22 da Usman Ubale dan shekara 26.
Jami’in hulda da jama’a ya yi nuni da cewa, an samu dukkanin mutane hudun a sume kuma daga baya aka tabbatar da sun mutu.
“An mika gawar su ga SP Abdulkadir M. Albasu na sashin ‘yan sanda na Dawanau domin ci gaba da bincike”.
Saminu ya ce, Daraktan hukumar kashe gobara ta jiha Alhaji Sani Anas ya jajantawa iyalan mamatan.
Ya kuma gargadi jama’a da su guji shiga cikin ruwa ba tare da izini ba ko kuma masu hadari, musamman wadanda ayyukan gine-gine ya shafa.
“Muna kira ga ‘yan ƙasa da su guji yin iyo ko wasa a cikin kududdufi, musamman waɗanda aka toshe ko ba a tsara su don amfani da nishaɗi ba.
Al’umma na ci gaba da nuna alhininsu yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan al’amuran da suka dabaibaye wannan mummunan lamari.
Rel/Khadijah Aliyu