Aragchi: Shirin Nukliyar Kasar Iran Na Tafiya Kan Fahintar Rashin Amincewa Da Babakere
Published: 31st, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ta gina shirinta na makamashin nukliya ne kan fahinta da kuma kundin tsarin mulkin kasar wanda yayi tir da mamaya da kuma babakere.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Asabar a hubbaren Imam Ruhullah Al-khomaini (q) wanda ya kafa JMI.
A cikin wani wuri a Jawabinsa Ministan ya kara da cewa a cikin kundin tsarin mulkin JMI ya zo kan cewa Iran ba zata danne wata kasa ba kuma ba zata amince da danniyaba, hakama ba zata zalunci wata kasa ba kuma ba zata yarda a zalunceta ba.
Ya ce abinda gwamnatin kasar Amurka take son tayiwa JMI shi ne danniya da zalunci, Kalmar kada ku ce makamacin Uranium kanta danniya ce. Su sun amincewa kansu su mallaki makaman nukliya amma ba zasu amincewa wata kasa ta ma tashe makamashin uranium wanda yarjeniyar NPT ta amince masu su tace ba. Don haka wannan baa bin amincewa ne ga JMI ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA