HausaTv:
2025-07-24@03:42:14 GMT

Masu Zanga Zanga A Libya Sun Bukaci Firai Ministan Kasar Ya Sauka

Published: 31st, May 2025 GMT

Masu zanga zanga kimani makunni uku da suka gabata a kasar Libya sun bukaci firai ministan kasar Abdulhamid Dubba ya sauka saboda shi ne ya haddasa rikicin da ya faru a cikin yan makonnin da suka gabata a kasar.

Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa masu zanga zanga kimani 200 sun taro a tsakiyar birnin Tripoli sun rera takin Dole Dubah ya sauka, wanda kuma suna rera wasu taken.

Tun shekara ta 2011 ne a lokacinda kungiyar tsaro ta nato ta goyi bayan yantawaye suka kashe shugaba Kaddafi ne kasar Libya ta rabu gida biyu, bangaren da MDD ta amince da ita a birnin Tripoli da kuma wacce Khalifa Haftar yake jagoranta daga gabacin kasar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh

Kimanin mutum 16 sun rasa rayukansu a ranar Litinin bayan wani jirgin rundunar sojin sama ta Bangladesh ya fadi a cikin harabar wata makaranta a Dhaka, babban birnin kasar.

Haɗarin jirgin saman yaƙin ya kuma yi sanadin jikkatar gommai, wanda ya kasance guda daga cikin haɗɗura masu muni da ƙasar ta gani a baya-bayan nan a fannin jiragen sama.

Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet Ƙalubalen da ke tattare da sauya sunan jami’a

Wani mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na AFP da ke wurin ya ce ya ga jami’an kashe gobara suna kwasar daliban da suka jikkata yayin da sojoji ke taimakawa wajen zakulo mutane daga cikin baraguzan jirgin da ya fadi.

Fiye da mutane 100 ne suka jikkata a hadarin, inda akalla 83 ke karbar magani a asibitoci daban-daban, in ji wani jami’i a ofishin gwamnatin kasar, Muhammad Yunus.

Bayanai sun nuna cewa waɗanda suka jikkata mafi yawansu ɗalibai na karɓar kulawar likitoci, yayinda wasu yayi munin da sai anyi musu gagarumar tiyatar sauya hallita.

Jirgin na F-7 BJI da aka kera a kasar Sin ya tashi ne da karfe 1:06 na rana (07:06 GMT) kuma ya faɗi mintuna kaɗan bayan da aka saki ɗaliban daga ajujuwansu don fita tara a harabar makarantar mai suna Milestone School and College.

Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda iyayen ɗaliban suka isa filin makarantar a ƙiɗime, don neman yaransu, amma wasu anan suka ci karo da gawargwakin yaransu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
  • Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
  • Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu
  • Karin Maganar Sinawa: Koyar Da Su Ya Fi Bayar Da Kifi
  • Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin
  • Libya Ta Tasa Keyar Baƙin Haure Yan Kasar Sudan 700 Zuwa Kasarsu
  • Ministocin Tsaron kasashen Rasha Da JMI Sun Hadu A Birnin Mosco