Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
Published: 23rd, March 2025 GMT
Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin halin da ake ciki a yakin da sojojin kasarsa suke fafatawa da gwamnatin kasar Amurka.
Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata aiko da jirgin ruwan yaki mai suna USS Carl Vession zuwa tekun Maliya don karfafa USS Harry Truman a yakin da take fafatawa da sojojin kasar Yemen.
Shugaban kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa sojojin kasar Yemen zasu ci gaba da abinda suka sa a gaba na maida martini kan jiragen yakin Amurka a tekun Red Sea da kuma dukkan jiragen HKI ko wadanda suke zuwa can don tallafawa mutanen Gaza.
Shugaban kasar Amurka donal Trump dai ya sha alwashin shefe kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen daga Doron kasa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Amurka kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp