NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci
Published: 24th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Hausawa sun yi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane su be kasuwa’.
Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikinsu na ɗaya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so.
Sai dai da zarar an ce watan Ramadana ya kama wasu daga cikin harkokin kasuwancin kan samu naƙasu, yayin da wasu kuma ke haɓaka.
Wasu kuwa kasuwar ce ke sauya salo, inda take dakushewa a wasu sa’anni ta kuma haɓaka a wasu sa’anni.
NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen GwamnaShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda wasu harkokin kasuwancin ke haɓaka da kuma yadda wasu ke samun koma baya cikin watan Azumin Ramadana.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Azumin Ramadan kasuwa Kasuwanci
এছাড়াও পড়ুন:
An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa
Yau Talata, kwamitin kwaskwarima da raya kasar Sin, ya fitar da kudin Sin RMB yuan miliyan 200, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 28, domin tallafawa wajen farfado da sassan birnin Beijing da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa, musamman ma fannin sake gina ababen more rayuwar jama’a na sufuri, da samar da ruwan sha, da kiwon lafiya, da na hidimomin al’umma a gundumomin Miyun da Huairou, a kokarin ganin rayuwa ta dawo kamar yadda take a wuraren, an kuma dawo da ayyuka kamar yadda aka saba.
Ban da haka kuma, ma’aikatar kudi, da ma’aikatar lura da ayyukan gaggawa ta kasar sun zuba kudin Sin yuan miliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 49 don tallafawa biranen Beijing, da Tianjin, da lardunan Hebei, da Shanxi, da Jilin, da Shandong, da Guangdong, da Shaanxi da jihar Mongolia ta Gida, ta yadda za su samu zarafin gudanar da ayyukan ceto, da rage radadin bala’u, da kuma taimakawa wadanda bala’in ya shafa. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp