Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [16]
Published: 24th, March 2025 GMT
Mataki na uku shi ne mutum ya so samun irin wannan ni’ima kamar yadda wani yake da ita, ba tare da yana so ta gushe daga hannun wanda yake da ita ba. Wannan kuwa ba hassada ba ce, sai dai ana kiranta da fatan alheri ga kai.” Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [4/226]
Fashin Baƙi:
Ibn Juzai al-Kalbi ya bayyana mana rabe-raben hassada.
● Matakin Farko na Hassada:
Shi ne mutum ya so wata ni’ima da Allah Ya ba wa wani ta gushe daga gare shi, ko da kuwa ba zai amfana da ita ba. Wannan shi ne mafi munin nau’in hassada gaba ɗaya, kuma yana ɗaya daga cikin manyan cututtukan zuciya da ke hana albarka a rayuwa.
Wannan nau’in hassada yana nufin mutum yana jin haushin samun wata ni’ima a hannun wani, ba don yana son ita ta koma gare shi ba, sai dai kawai ya ƙi ganin wani yana da ita. Wannan yana iya kasancewa a cikin kowace irin ni’ima, kamar:
• Dukiya da arziki
• Matsayi ko shugabanci
• Ilimi da hikima
• Kyakkyawar rayuwa
Farin ciki da kwanciyar hankali da sauran su.
A wasu lokuta, mai irin wannan hassadar ba shi da watbuƙata a kan ni’imar da yake hassada, amma kawai yana jin cewa wannan mutumin bai cancanci wannan alheri ba. Wannan yana nuna kyashi da mugunta a zuciyar mai hassadar.
Alamomin Wannan Hassada:
Jin haushin duk wani alheri da wani ya samu.
Ƙin fatan wani ya cigaba ko ya sami wadata ko farin ciki. Idan ya ga wani yana cikin alheri, yana jin haushin hakan. Idan wannan ni’ima ta gushe daga hannun mai ita, sai ya ji daɗi. Baya iya ɓoye jin haushinsa idan wani ya sami nasara ko farin ciki.
Misalan Irin Wannan Hassada:
1. Hassadar Iblis ga Annabi Adam (AS): Labarin farko da ya nuna irin wannan hassadar shi ne na Iblis da Annabi Adam (AS). Allah Ya ba Adam matsayi na musamman, amma Iblis ya ƙi yarda, yana jin haushin Allah Ya ba wa Adam daraja. Bai so ya zama kamar annabi Adam (AS), sai dai kawai ya ƙi ganin annabi Adam yana da wannan matsayi har yana cewa:” Yanzu na yi sujjada ga wanda Ka halitta da taɓo?” Suratul Isrã’i aya ta 61. Iblis bai buƙaci wannan matsayi ya koma gare shi ba, amma bai son annabi Adam (AS) ya ci gaba da kasancewa a ciki ba. Wannan ita ce hassada mafi muni.
2. Hassadar Yahudawa ga Musulumi:
A cikin suratul-Baƙara, Allah Ya bayyana cewa Yahudawa sun yi hassada ga Musulumi saboda Allah Ya ba su addinin da ya fi na su. Sun san gaskiya, amma sai suka ƙi amincewa da ita saboda hassada. Allah Ta’ala Ya ce:” Da yawa daga ma’abota littafi sun yi burin jna ma a ce su mayar da ku kafirai bayan imaninku, saboda hassada daga zukatansu, bayan kuma gaskiya ta bayyana a gare su.” Suratul-Baƙara aya ta 109.
Ba don Yahudawa suna son addinin Musulunci ya kasance nasu ba, sai dai kawai suna jin haushin Musulumai sun samu wannan ni’ima.
3. Hassadar ‘Yan’uwan Annabi Yusuf (AS):
‘Yan’uwan Annabi Yusuf sun yi hassada a kansa ba don suna son su zama Annabawa ba, sai dai kawai sun ƙi ganin mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da su. Saboda haka, suka nemi hanyar raba shi da wannan ni’ima. Allah Yana cewa:” Ka tuna lokacin da ‘yan’uwan suka ce:” Lalle Yusufu da ɗan’uwansa babammu ya fi son su da mu, ga mu kuwa jama’a masu yawa. Lalle babammu yana cikin kuskure mabayyani.” Suratu Yusuf aya ta 8.
Suna ƙyamar ganin annabi Yusuf yana cikin soyayyar mahaifinsu, har suka yi ƙoƙarin halaka shi. Wannan yana nuna yadda hassada take kai mutum ga zalunci da cutar da wasu.
4. Illolin Wannan Hassara:
Rashin Yarda da Ƙaddarar Allah: Wannan nau’in hassada yana nuna cewa mutum bai yarda da yadda Allah Yake rabon ni’ima ba. Mai irin wannan hali yana ƙin hikimar Allah da yadda Ya tsara rayuwa.
Rashin Farin Ciki da Kwanciyar Hankali: Mutum mai irin wannan hassada yana cikin damuwa a koyaushe. Yana ƙunci idan ya ga wani cikin alheri, yana fushi idan wani ya sami nasara, kuma yana jin baƙin ciki idan wani yana da wadata.
Yana Haifar da Gaba da Ƙiyayya a Tsakanin Mutane: Hassada tana haddasa gaba da ƙiyayya a tsakanin mutane. Mai irin wannan hali baya son ci gaban wasu, wanda hakan ke haifar da matsaloli a cikin al’umma.
Rashin Albarka a Rayuwa: Mutumin da yake da irin wannan hassadar ba ya samun albarka a rayuwarsa, domin Allah ba Ya albarkantar da zuciya mai kyashi da mugunta.
Allah Ya yi mana katangar ƙarfe da hasaada. Amin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan irin wannan hassada mai irin wannan Wannan Hassada sai dai kawai wannan ni ima Allah Ya ba
এছাড়াও পড়ুন:
’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
An ceto dukkanin mutane 14 ba tare da wani ya ji rauni ba, amma abin baƙin ciki, wani matashi ɗan shekara 27 mai suna Abba daga garin Funtua ya rasa ransa kafin isowar ’yansanda.
A wani lamari da ya faru a ranar 28 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 11:27 na dare, an sake kiran ’yansanda daga ƙauyen Zagaizagi, inda aka sanar da su cewa wasu ’yan bindiga sum hari tare da sace wasu mutane ƙauyen.
’Yansanda sun isa wajen suka gwabza da ’yan bindigar, kuma sun samu nasarar ceto wasu mutane 14 da kuma ƙwato shanun da aka sace guda biyu.
Amma, mutane biyu daga cikin mazauna ƙauyen sun rasa rayukansu a harin.
Rundunar ta ce har yanzu tana ci gaba da ƙoƙarin kamo ’yan bindigar da suka tsere.
Kwamishinan ’yansandan, CP Bello Shehu, ya yaba wa jami’ansa bisa jarumtaka da suka nuna.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa ’yansanda sahihan bayanai a kan lokaci.
Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp