Leadership News Hausa:
2025-09-24@15:44:07 GMT

Azumi Ya Dara Wa Sauran Ibadu

Published: 21st, March 2025 GMT

Azumi Ya Dara Wa Sauran Ibadu

Shi wannan azumi, na wani lokaci ya fi na wani lokaci kamar an so a dinga yin azumi sau Uku a cikin kowanne wata, lokacin kwanan wata yana 13 da 14 da 15, wannan kwanaki hasken wata ya fi haske a cikinsu, to kamar yadda suke haske haka zuciyarka za ta kara haske sabida saduwa da hasken, sannan kuma hawa-hawa na musulunci guda Uku ne (Islam da Iman da Ihsan) to wanda ya riski wannan kwanaki Uku kamar Ya hau dukka wannan Matakan addinin ne.

Akwai azumin Litinin da Alhamis, azumin ranar Litinin Annabi (SAW) ne yake yi, an tambaye shi cewa Ya Rasulullahi sabida me kake azumin ranar Litinin? sai ya ce ranar ce aka haife ni, ina godiya ga Allah. To duk wanda ya yi azumin ranar Litinin ya yi koyi da Annabi (SAW) ne. Azumin ranar Alhamis kuma, Annabi (SAW) ya ce ranar ake nade ayyukan bayi na mako zuwa ga Ubangijinsu Rabbul Izzati, ina kwadayin a kai aikina ga Ubangiji ina azumi. Akwai sauran azumomin nafila da yawa.

Akwai babban azumin nafila da ake cewa ‘Na Annabi Dawudu’: Annabi Dawudu Mutum ne sarki mai ibada, yana daga cikin Ibadarsa azumi. In ya yi azumi yau, gobe sai ya ci abinci, haka ya kasance yanayi a rayuwarsa, idan ya rayu shekaru 60 – shekaru 30 ya yi azumi.

Allah yana gode wa Dan’adam in ya ce zai yi azumi duk ranar da yake so sai dai ba a so ya ware wata rana kamar Jumu’a ko Asabar ya dinga azumtarsu duk sati. Lallai azumi yana da falala sosai.

Allah ya wajabta mana azumi kamar yadda ya wajabta ma wadanda suka zo kafin mu.
An karba hadisi daga Mu’azu bin Jabal yana cewa: “Manzon Allah (SAW) bayan ya yi Hijira zuwa Madina, sai wata rana, Yahudawan Madina duka suka tashi da Azumi – Ashura, sai Annabi (SAW) Ya tambayesu lafiya, sai suka ba shi amsa da cewa ai wanna ranar ce Allah ya tseratar da Annabi Musa ya hallakar da Fir’auna, sai Annabi (SAW) yabce mu muka fi cancanta da Musa”. Annabi (SAW) ya yi umarnin cewa kowa ya ci gaba da azumin, shekara mai zuwa Allah ya saukar da azumin watan Ramadana, Annabi (SAW) ya ce Allah ya ba mu namu wanda ya so ya ci gaba da na Ashura, har Annabi (SAW) ya koma ga Allah yana azumin Ashura, azumin yana daga cikin manyan azumin Nafila a addinin Musulunci.

Ya zo cewa Annabi (SAW) ba ya barin azumin kwana Uku na kowanne wata. Idan mutum yana yin azumin kwana Uku na kowanne wata za a rubuta masa ladan kwana 30, sabida kowanne aiki daya ana rubuta masa goma, don haka azumin kwana uku dai-dai yake da uku sau Goma, Talatin kenan.

Allah ya wajabta azumin Watan Ramadana ga al’ummar musulmi bakidaya, amma a farko masu hali (dukiya) ciyarwa suke, marasa dama kuma su yi azumi, har sai da Allah yace “Wa’anta sumu khairullakum” sannan ya zama wajibi a kan kowa. Amma har gobe, yana nan marasa lafiya su kididdige kwanukan da suka tsere musu su biya a wasu ranaku bayan watan Ramadana, wadanda ba za su iya azumtar watan ba su ciyar, matafiyi in ba zai iya azumi cikin tafiyar ba, shi ma ya ciyar.

Yana daga cikin falalar watan Ramadana, Annabi (SAW) ya ce idan Watan Ramadana ya zo, duk kofofin Aljannah bude su ake yi, duk kofofin wuta kuma sai a kulle, kuma sai a kulle duk shaidanu, sai ka ga masallatai duk sun cika, sabida abokin yawon shaidancin an kulle shi. Ba ana nufin Aljannu da suke kama mutane ba na rashin lafiya, wannan ciwo ne, lada za a bai wa majinyacin, abokin yawon shaidancin ake daurewa.

Nasa’i ya ruwaito cewa kullum mai kira zai yi kira a cikin dare, yana cewa “ya kai mai neman alheri taho, ga watan alheri ya zo, ya kai mai neman sharri kame, wannan ba watan sharri ba ne.”

Wasu daga cikin Malamai sun tafi cewa ‘Ramadana’ sunan Allah ne sabida Hadisin Abi Hurairah da yake cewa “kar ku ce Ramadana ya zo, sabida Ramadana suna ne daga cikin sunayen Allah”. Allah a Littafinsa cewa ya yi “Shahru Ramadana…” Amma ba laifi in an ce Ramadana ya zo sabida ana nufin watan Ramadana.

Allah ya saukar da mafificin littafi (Alkur’ani) a cikin watan Ramadana, a mafificin dare (Lailatul Kadri).

An karba daga Abdullahi bin Abbas, Allah ya yarda da su, yake cewa “Allah Ya saukar da Alkur’ani daga lauhil mahfuzi izuwa saman Duniya (a cikin Ramadana aka saukar da alkur’ani daga lauhil mahfuzi zuwa saman Duniya, a dakin Baitul ilimi), Mala’ika Jibril (AS) shi kuma daga nan yake debo ayoyinsa zuwa ga Annabi (SAW), sai da ya shafe shekaru 23 yana kan wannan aikin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: watan Ramadana azumin ranar

এছাড়াও পড়ুন:

Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau

Mataimakin shugaban jami’ar ya ja hankalin gwamnati da cewa, yawan al’ummar Nijeriya kusan miliyan 230, kusan kashi 30 cikin 100 na matasa ne a halin yanzu ke makaranta ko kuma suke koyon sana’o’i.

 

Don haka, ya yi gargadin cewa, hakan ya bar wani kaso mai tsoka na matasa da ba su zuwa makaranta ko ba su da aikin yi, – lamarin da ya bayyana a matsayin “abin takaici da haɗari ga al’ummarmu.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yada labaran karya a intanet babban laifi ne a Musulunci – Sheikh Ibrahim Khalil
  • Larijani: Donald Trump Yana A Matsayin Makwafin Adolf Hitler
  • Larijani: Iran na kare tsaron kasa da azama
  • Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82
  • DSS ta yi wa Malami tambayoyi kan harin da aka kai masa a Kebbi
  • Faransa ta amince da ’yancin ƙasar Falasɗinu a hukumance
  • Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau
  • Sarkin Ruman Katsina ya rasu
  • Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano
  • Yadda Wasu Mata Ke Gwada Mazansu Ta Hanyar Magana Da Su Ta Wasu Hanyoyi Don Sanin Ku Suna Kula Mata