Eid-el-Fitr: Sarkin Kauru Ya Gargadi Masu Bai Wa ‘Yan Ta’adda Bayanai
Published: 31st, March 2025 GMT
Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare.
Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman na biyu, ya jaddada muhimmancin hadin kai wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a lokacin da ya gabatar da sakon Sallar a fadarsa da ke Kauru.
Alhaji Zakari Ya’u Usman ya kuma yi gargadi game da masu ba da labari da ke taimaka wa masu laifi tare da karfafa gwiwar mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi.
Dangane da harkokin kiwon lafiya, Sarkin ya bukaci iyaye da su ba da fifiko ga allurar rigakafin yara don kare su daga cututtukan da za a iya rigakafin su.
Ya kuma shawarci mata masu juna biyu da su rika zuwa duba lafiyarsu akai-akai, sannan ya shawarci jama’a da su nemi kulawar lafiya a kan lokaci domin rage kamuwa da cututtuka kamar hawan jini da ciwon suga.
A cewarsa, Masarautar ta nuna godiya ga gwamnatin jihar kan aikin hanyar Pambeguwa zuwa Kauru da kuma tallafawa manoma ta hanyar rabon taki. Sai dai Sarkin ya roki a kara ayyukan hanyoyin da suka hada da Kauru zuwa Mariri a karamar hukumar Lere, Unguwan Ganye zuwa Dokan Karji mai hade da Kasuwan Magani a karamar hukumar Kauru, da kuma titin mai tsawon kilomita 10 a cikin garin Kauru.
Ya kuma bukaci a kammala kashi na biyu na gyaran fadar Kauru, musamman a wuraren da ke bukatar kulawar gaggawa, musamman a lokacin damina.
Sarkin ya yi addu’a don ci gaba da zaman lafiya da wadata a shekaru masu zuwa.
Hakazalika, Sakataren Masarautar, Malam Muhammad Sani Suleiman (Danburan Kauru) ya nuna jin dadinsa ga wadanda suka halarci bukukuwan Sallah tare da jajantawa iyalan wadanda rashin tsaro ya shafa.
COV/Yusuf Zubairu Kauru
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yan Ta adda Bayanai Gargadi Sarkin Kauru
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.
Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11.
Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu.
NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuA kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan