2025-10-13@15:53:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2384

«Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe»:

    Mai kuɗin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa. Ɗangote ya yi zargin cewa miyagun ’yan kasuwan suna ƙoƙarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masana’antar tufafi ta ƙasar. Ya bayyana haka ne...
    Sojoji biyu sun ji rauni bayan wani harin kwanton baya da ’yan bindiga suka kai kan ayarin motocin Kwamandan kwamandan Rundunar Sojoji ta 382 Ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ruwan Godiya, kan hanyar Sheme–Kankara, lokacin da tawagar Operation Fansan Yamma (OPFY) ke wucewa. Ganau sun ce sojojin na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a...
    Ministan tsaro na kasar Venezuela Vladimir Padrino López ya gargadi gwamnatin Amurka dangane da duk wani kokari na kaiwa kasar Venuzuela hare hare saboda kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Madoro. Tare da fakewa da fasakorin kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Vladimir yana cewa take-taken gwamnatin Amurka na sojojin da ta...
    Shugaban kasar Iran yana mai jaddada cewa wajibi ne kasashen musulmi su karfafa hadin kai da hadin kai don mayar da martani ga ayyukan gwamnatin sahyoniyawan, inda ya ce: Wajibi ne kasashen musulmi su tsaya tsayin daka tare da daukar matakai na zahiri a fagen tattalin arziki, al’adu da zamantakewa, yanke alakarsu da gwamnatin sahyoniyawan....
    Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur. Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki. Har ila yau, ya ce an biya bashin da...
    “Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.   Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel...
    Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.   Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa...
    A yau Litinin ne dai kungiyoyin kasashen musulmi da na larabawa su ka yi taron gaggawa a birin Doha na kasar Qatar da aka tattauna harin wuce gona da iri da HKI ta kai wa kasar. Bayanin bayan taron ya kunshi bangarori mabanbanta da su ka hada da daukar matakai kwarara domin taka wa HKI...
    Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.   Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne...
    Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta shiga tsakani don sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO). Rikicin ya samo asali ne daga katse wutar lantarki da asibitin ya zargi KEDCO da yi, inda ya ce hakan ya kawo cikas ga ayyukan...
    Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.   Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne...
    Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi. A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun...
    Ministan harkokin wajen Iran ya gana da takwarorinsa na Qatar, Turkiyya, Pakistan da Lebanon a Doha fadar mulkin kasar Qatar Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da takwaransa na Qatar a gefen taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Doha. Doha ta sanar da cewa, fira ministan...
    Kwamitin koli na tsaron kasa ya amince da yarjejeniyar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya yi gargadin cewa, idan aka dauki wani mataki na nuna adawa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cibiyoyinta na makamashin nukiliya, ciki har da sake farfado da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar...
    Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa,...
    A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara. A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.   Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11. Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Shawarar tsarin shugabancin duniya” ta zama kalmar da aka sha karanta a rahotannin kafofin watsa labaru na duniya cikin kwanakin baya. Shugabannin wasu kasashe da dama suna ganin cewa, wannan shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron koli na SCO da aka gudanar a kwanan baya a birnin Tianjin, tana...
    An karrama fitattun fina-finai daban daban a bikin “Golden Panda” da ya gudana jiya Asabar a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kasar Sin. A bana, an gudanar da bikin ne a karo na biyu, wanda kuma gungun sassan bunkasa harkokin adabi da al’adu da gwamnatin lardin Sichuan suka dauki nauyin shirya shi. Bikin na...
    A cikin sanarwarsa, Daso ya ce: “Rundunar Ƴansanda ta Jihar Borno na sanar da jama’a cewa an gano gawar wani mutum da ba a tantance ba a kusa da na’urar sauya wuta (transformer) a Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri. “Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya mutu ne sakamakon jan wutar lantarki yayin da yake ƙoƙarin...
    Hakazalika, sojojin na Brigade 12 tare da hadin gwiwar dakarun hadin gwiwa da ’yan banga a wannan rana, sun ceto fasinjoji 17 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi.   Hakazalika, dakarun Sashe ta 1 ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’ sun ceto wani a karamar hukumar Katsina-Ala...
    Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa. Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan...
    Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin...
    Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar...
    Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da...
    Tsohon kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mosen Razai ya bayyana cewa kasashen yanking abas ta tsakiya su saurari fadowar boma boman HKI a kan kasashensu idan sun ki daukar matakin hada kai da kuma samar da rundunar kawance don fuskantar haramtacciyar kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rezayi yana fadar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya sanar da yiwuwar sake yin wani taro da babbar jami’ar kungiyar tarayyar Turai kan harkokin waje Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da yiwuwar sake ganawa da babbar jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Kaya Kalas. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya...
    Shugaban rikon kwaryar Siriya ya bayyana cewa; Babu sabani na dindindin da Iran Shugaban rikon kwarya na Siriya Abu Mohammed al-Jolani ya yi magana kan alakar Siriya da sauran kasashe, inda ya mai da hankali kan Rasha, Iran da Masar. Ya kuma yi jawabi game da zaben Siriya da ayyana kundin tsarin mulkin kasar da...
    Wike ya goyi bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani mataki da ya samu matsayin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. Duk da yake har yanzu shi mamba ne na PDP, Wike ya kasance yana bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar yayin da yake kuma yin aiki don sake zaɓen Tinubu, wani...
    Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma. “Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai. Ina...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Bai kamata a ji tsoron tattaunawa ba saboda hanya ce ta jaddada zaman lafiya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Ana gudanar da dukkan ayyukan diflomasiyya cikin cikakken hadin kai tare da hukumomin da abin ya shafa, kuma bisa takamaiman umarni da ayyuka. Ya...
    Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za...
    “Direban ya yi nasarar tserewa, amma sun harbi motar, inda Zakari Benjamin da Samaila suka samu raunuka a ƙafafu,” in ji shi. ‘Yansanda daga Kontagora sun isa wajen da abin ya faru, sannan suka kai waɗanda suka ji rauni asibiti. Abiodun ya ƙara da cewa an tura jami’an tsaro zuwa wajen, amma ‘yan bindigar sun...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da miƙa ƙudirin doka ga Majalisar Dokokin Jihar domin haramta auran jinsi da kuma wasu aiyukan batsa a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 31 da aka gudanar a ofishin gwamnati na birnin Kwankwasiyya. A wata sanarwa da...
    Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24 ba tare da ɗaukewa ba. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya ƙaddamar da sabbin ɗakunan horo da ɗakin kwana a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Ƙasa (NAPTIN). Gwamna ya...
      Wanna taro yana da matukar muhimmanci, taro ne na murnar Annabi SAW, taro ne da haka Halitta ta saba. Duk al’umma tana farin ciki da murnar haihuwar wani mai girma acikinsu, ko wani wanda ya kawo musu cigaba ta hanyar rayuwa ko cigaba ta hanyar kasarsu ko kowa ma yana murnar ranar haihuwarsa, kamar...
    Gwamnatin jihar ta sha alwashin bayyana sakacin aikin da Kwamishinan ya yi da zarar ta kammala bincike.   Don haka, an umurci  babban jami’i a ma’aikatar da ya ci gaba da jan ragamar ayyukan ma’aikatar har zuwa lokacin da za a fitar da wata sabuwar sanarwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    A cewarsa, kudaden fansa da ake yawan ji ana biya yawanci iyalan wadanda abin ya shafa ko al’ummarsu ne ke tarawa.   Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira biliyan 2.5 a shekarar 2025 kadai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka.  ...
    A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta soki lamirin harin da aka kaddamar a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar a jiya Talata, tana kuma adawa da matakin Isra’ila na cin zarafin ikon mulkin...
    Zanga-zangar matasa a Nepal, da aka ƙirƙira a matsayin “Gen Z Revolution,” ta ɓarke ne da nufin ƙalubalantar rashawa da takunkumin amfani da kafofin sada zumunta, sai dai ta rikiɗe zuwa tarzoma mai muni. Rahotanni sun bayyana cewa, an fara zanga‑zangar ne sakamakon hana amfani da manyan kafafen sada zumunta guda 26, ciki har da...
    Haka zalika, Ministan Ilimi, Dakta Olatunji Alausa , shi ma ya jinjinawa rawar da Gwamna Sani ya taka wajen sauƙaƙa bikin kaddamar da Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar, yana mai cewa yanzu haka ana sake fasalin makarantun fasaha na ƙasa baki ɗaya domin su mai da hankali...
    Rabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, ta rasu bayan masu zanga-zanga sun banka wa gidansu wuta a unguwar Dallu da ke birnin Kathmandu a ranar Talata. Bayanai sun ce masu zanga-zanga a ƙasar mai tsaunuka da ke fama da tashin hankali mafi muni cikin shekaru da dama sun tarfa matar tsohon firaministan...
    Jiragen yakin HKI sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a yau Laraba, inji tashar talabijin ta Al-Masirah na gwamnatin kasar. Labarin ya kara da cewa yahudawan sun kai hare-haren ne a tsakanin wasu duwatsu a cikin kasar, da kuma kan cibiyar kungiyar Ansarullah da ke tsakiyar birnin San’a babban birnin kasar, da kuma ma’aikatar...
    Bisa amincewar majalisar gudanarwar kasar Sin, gwamnatin kasar za ta kafa yankin kare muhallin halittu na Huangyan Dao. Tuni dai aka fitar da sanarwar amincewa da hakan a shafin yanar gizo na gwamnatin tsakiyar kasar Sin, wato www.gov.cn a Larabar nan, bayan da ma’aikatar kare albarkatun kasa ta gabatar da bukatar hakan. Sanarwar amincewa da...
    Yayin da aka gano gawar Surajo a ranar Litinin, an gano gawar Fatima washegari, Talata. Sai dai har yanzu ba a gano gawar kanwar Fatima ‘yar shekara uku, Haneefa ba.   A lokacin da lamarin ya faru, Fatima tana goye da kanwarta Haneefa mai shekaru uku a duniya.   Su biyun suna dawowa ne daga...
    Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023, Rabiu Kwankwaso, a ranar Talata ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kuros Ribas domin tsara dabarun tunkarar babban zabe na 2027. Da yake jawabi a babban birnin jihar, Kalaba, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ba...
    “Wannan matakin ya zama dole don dakatar da saran gandun daji, kare muhalli, da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa,” in ji Dokta Hashim.   Ya yi gargaɗin cewa, duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri. “Za a tsaurara doka, tare da biyan tarar ₦500,000 da kuma yiwuwar ɗauri a gidan yari saboda...
    Onuh ta ce, “Ba zai yi wu ba, mu bar ayyukanmu, da yawa daga cikinmu sun yanke hutun da suke kai, muka taho daga Legas saboda wannan zama amma Ministan ya yi watsi da kiran majalisar.   “An jefa ‘yan’uwanmu cikin hatsari, wannan ba abun wasa ba ne, don haka mun dakatar da taron kuma...