Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan a Jama’iyyar ADC
Published: 24th, November 2025 GMT
A yau Litinin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, zai yankin kati domin shiga Jam’iyyar ADC a hukumance.
Manyan hidiman Atiku sun shaida wa Aminiya cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin yin rajistar Atiku a mazaɓarsa ta Jada 1 da ke Ƙaramar Hukumar Hada ta Jihar Adamawa.
Atiku ya yi nuni da wannan mataki ne a wani taro da ya gudanar da shugabannin ADC na Jihar Adamawa a Yola, inda ya ce: “A Najeriya gaba ɗaya akwai sabon motsi na siyasa, ko ba haka ba? Yau wannan motsi ya kai mu ina? ADC.
Ya ƙara da cewa: “Bayan haka, a ranar Litinin zan kasance a hukumance cikin ADC. Kafin yanzu ban shiga ba; ku ne kuka riga ni. Za ku karɓe ni?”
Tun da farko ana ta shakku kan irin jajircewar Atiku da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Lam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, ga ADC, bayan da ƙungiyar adawa da suke jagoranta ta amince da jam’iyyar a matsayin dandalin ta na zaben 2027.
Rashin halartar Atiku da Obi wajen ƙaddamar da sabuwar hedikwatar ADC a makon da ya gabata ya ƙara haifar da tambayoyi kan ko suna nan daram da matsayar ƙungiyar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: rajista
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro.
Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta NejaMai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba.
Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar kowane bayani kafin su yaɗa shi domin kauce wa yaɗs labarun ƙarya.
Wannan bayani ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya na rufe manyan makarantun sakandare 41 da ke yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro, sakamakon sace ɗalibai a jihohin Neja da Kebbi.
Haka kuma wasu jihohi kamar Kwara, Filato, Katsina da Neja sun rufe makarantunsu saboda matsalar tsaro.
Jihar Taraba ma ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu da ke jihar.