Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya
Published: 23rd, November 2025 GMT
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan sanda umarnin daina tsaron manyan mutane a faɗin Najeriya.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi.
’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a BauchiOnanuga, ya ce daga yanzu ’yan sanda za su mayar da hankalinsu ne aikin kare al’umma da yaƙar ’yan ta’adda.
An ɗauki wannan mataki ne a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja, wanda manyan shugabannin tsaro suka halarta, ciki har da shugabannin ’yan sanda, sojin sama, sojin ƙasa da hukumar DSS.
Sabon tsarin ya nuna cewa duk wani babban mutum da yake buƙatar tsaro dole ne, ya nemi jami’an tsaro daga Hukumar NSCDC maimakon ’yan sanda.
Najeriya ba ta da isassun ’yan sanda a yankunan karkara, kuma hakan yana haifar da tsaiko wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Saboda haka Shugaba Tinubu, ya umarci a ƙara yawan ’yan sandan da ke bai wa jama’a tsaro.
Onanuga, ya kuma ce Shugaban Ƙasa ya amince da ɗaukar ƙarin sabbin ’yan sanda 30,000.
Gwamnatin Tarayya za ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi domin inganta cibiyoyin horas da ’yan sanda a faɗin Najeriya.
Taron tsaron da aka gudanar a ranar Lahadi, ya samu halartar Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da Darakta-Janar na DSS, Tosin Adeola Ajayi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda manyan mutane Tsaro umarni
এছাড়াও পড়ুন:
Madagascar: An Bayyana Jadawalin Farko Na Gwamnatin Rikon-Kwarya Da Kuma Manyan Zabuka
Fira Ministan kasar Madagascar Herintsalama Rajaonarivelo ya gabatar da jadawalin ayyukan siyasa a gaban majalisar kasar, da a ciki ya kunshi yadda zaman gwamnatin rikon kwarya zai kasance da yadda zai kai ga yin manyan zabukan kasar a cikin shekara daya da rabi.
Fira ministan kasar ta Madagascar ya kuma ce; A karshen watan farko na gwamantin rikon kwarya ne za a bude ttataunawa a fadin kasar, wanda kuma zai ci gaba har tsawon watanni shida. Daga nan kuma za a bude tataunawa akan madogarar shari’a da yi wa hukumar zaben kasar kwaskwarima.
Bugu da kari, fira ministan ya ce, gwamantin rikon kwaryar za ta so shirya zabuka bayan watanni 14 zuwa 20 daga hawanta karagar Mulki.
Dangane da matsalolin da su ka fi damun al’ummar kasar, Fira ministan ya ce, suna son ganin an warware su a cikin lokaci mafi karanci, daga ciki da akwai matsalolin ruwan sha da na lantarki da kuma fari da ake fama da shi. Haka nan kuma matsalolin karancin abinci da mutanen kudancin kasar da kuma kudu maso gabashi suke fuskanta.
Wasu daga cikin batutuwan da gwamnatin rikon kwaryar take son magancewa cikin lokaci mafi karanci da akwai dawo da doka da tabbatar da tsaro da aiki da dokoki.
GWamnatin kasar ta rikon kwarya tana son gamsar da bukatun al’ummar kasar da su ka yi boren da ya kai ga kifar da gwamnatin Rajolina.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Unifil: Girmama Hurumin Kasar Lebanon Ne Ginshikin Kuduri Mai Lamba 1701 November 22, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 160 November 22, 2025 Duniyarmu A Yau: Sabon Kuduri Mai Yin Allawadai Da Iran A Hukumat IAEA November 22, 2025 Ghalibaf: Makiya Sun Sawya Dabarbarun Yaki Da Iran November 22, 2025 Tsohon Ma’aikacin CIA Ya Ce HKI Ta Yi Barazanar Amfani Da Makaman Nukliya Kan Iran November 22, 2025 Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Sami Rarrabuwar Kai Dangane Da ‘Keshe Kiristoci A Najeriya’ November 22, 2025 Kasar Ukraine Ta Ki Amincewa Da Sabon Shirin Amurka Na Kawo Karshen Yaki A Kasar November 22, 2025 Yan Wasan Kasar Iran Sun tashi Da Lambobin Yabo 81 A Wasannin Zumunci Tsakanin Kasashen Musulmi November 22, 2025 Shugaban Rasha yace Ba zai Janye Ayyukan Soji Da Yake Yi A Kasar Ukrain Ba November 21, 2025 Kwamitin Sulhu Na MDD Ya yi Tsokaci Kan Rashin Tsaro A Najeriya November 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci