Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi
Published: 25th, November 2025 GMT
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 13 da rabi, da ya tashi daga Sada zuwa Danakari zuwa Unguwar Malam Kuda, zuwa Magina, a Karamar Hukumar Yankwashi ta jihar.
A jawabinsa wajen bikin kaddamarwar, Namadi ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da muhimman abubuwan more rayuwa a karkara domin inganta harkokin tattalin arzikinsu.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Umar Namadi ya ce titin, wanda aka gina akan kudi Naira biliyan 1 da miliyan 690, na daga cikin manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi 48 da gwamnatinsa ta bayar a shekarar 2024.
A cewarsa, titin zai hada al’ummomin karkara na Sada, Danakari, Unguwar Malam Kuda da Magina.
Ya jaddada cewa mutanen wadannan yankuna sun daɗe suna bukatar wannan aiki na hanyar.
Malam Umar Namadi ya ce titin zai ba su damar kai amfanin gonakinsu kasuwanni mafi kusa cikin sauki.
Ya kuma ce yawancin wadannan hanyoyi sun kai matakin kammaluwa, kuma nan ba da dadewa ba za a gudanar da jerin bukukuwan kaddamar da su gaba daya.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da hanyoyin sufuri a karkara domin saukaka samun hanyoyin shiga kasuwanni da birane.
Namadi ya bayyana cewa shirin tuntubar jama’a ya bai wa al’umma damar tattaunawa kai tsaye da gwamnati.
Tun da farko, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na jihar, Injiniya Gambo Malam, ya ce titin na daga cikin hanyoyi 48 masu dauke da jimillar tsawon kilomita 977 da aka bayar a 2024 a kan kudi Naira biliyan 304.
Wasu daga cikin mazauna yankin, Malam Abdullahi Musa da Malam Muhammad Gata, sun yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan aiki.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja Ta Rufe Makarantu Saboda Matsalar Tsaro
Daga Aliyu Lawal
Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da na masu zaman kansu a fadin jihar sakamakon sace dalibai da aka yi a Makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Karamar Hukumar Agwara.
Gwamna Mohammed Umar Bago ne ya sanar da hakan a Minna bayan wata tattaunawar tsaro gaggawar ta da aka gudanar da shugabannin hukumomin tsaro, malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce matakin ya zama wajibi domin kare rayukan dalibai yayin da ake kara kokarin ceto yaran da aka sace.
Gwamna Bago ya jaddada cewa yanzu lokaci ne na daukar mataki a maimakon zargin juna, inda ya bayar da umarnin cewa a rufe dukkan makarantun mishan, da na Islamiyya da kuma kwalejojin gwamnati na tarayya har sai wani lokaci.
Haka kuma ya umurci a rufe dukkan manyan makarantu da ke yankin Neja ta Arewa da wasu yankuna masu hadari a Neja ta Gabas.
Gwamnan ya bukaci hukumomin tsaro, kungiyoyin fararen huhula, na kwadago da shugabannin addini su mayar da hankali wajen aikin ceto, yana mai tabbatar da kudirin gwamnati na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Yayin da yake bayyana lamarin a matsayin “abin bakin ciki da takaici,” Gwamna Bago ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da yin addu’a.
Ya ce har yanzu ba a tabbatar da yawan daliban Makarantar St. Mary’s Catholic School da aka sace ba, domin jami’an DSS, Rundunar ‘Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro na kan aiki don tantance sahihin adadin daliban da abin ya shafa.