Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-27@13:46:07 GMT

Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya

Published: 27th, November 2025 GMT

Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya

Daga Bello Wakili

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami.

Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101.

Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.

Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.

Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023.

“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima. A matsayinaa na mai wa’azi kuma masani kan tafsirin Alƙur’ani Mai Girma, yana da’awar zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.

Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga mabiyan Shehun a ci da wajen ƙasa  bisa wannan babban rashi.

Haka kuma ya ja hankalinsu da su girmama sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, ƙarfafa dangantakarsu da Allah, da kuma kasancewa masu taushin zuciya ga jama’a.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Ta aziyya

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka

An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar.

A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira.

Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar.

A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto.

“Addu’o’inmu suna tare da waɗannan jarumai, iyalansu, da dukan al’ummar Amurka.”

A cewar rahotanni, Shugaba Donald Trump yana gidansa na hutu a Mar-a-Lago da ke Palm Beach, Florida, a lokacin da lamarin ya faru.

Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce cikin wata sanarwa: “Fadar White House ta san da wannan mummunan lamari kuma tana bin diddigi. Shugaban kasa ya samu cikakken bayani.”

’Yan sandan birnin Washington DC sun ce an kama wanda ake zargi da harbin.

Sojojin National Guard sun kasance a Washington DC tsawon watanni a matsayin wani bangare na matakin Trump na yaki da laifuka a babban birnin ƙasar.

A cikin wani rubutu a dandalinsa na Truth Social, Trump ya ce: “Dabban da ya harbi mambobin National Guard biyu, wanda dukkansu suka ji rauni mai tsanani kuma yanzu suna a asibitoci daban-daban, shi ma ya ji rauni sosai, amma duk da haka, zai ɗanɗana kuɗarsa.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
  • Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani
  • Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa
  • Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka