Sace ɗalibai: Ba rufe makarantu ba ne mafita — PDP
Published: 24th, November 2025 GMT
Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu.
A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.
“Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji Ememobong
Ya ci gaba da cewa, “Idan aka rufe makarantu, to ’yan ta’adda sun cimma nasara.”
Umarnin janye ’yan sanda daga faɗin manyan mutane na iya zama magana kawai —Shehu Sani Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan a Jama’iyyar ADCYa buƙaci gwamnati ta samar da tsari na musamman don magance matsalar tsaro, maimakon sauƙaƙa ta, ta hanyar rufe makarantu don kauce wa sace-sace da kuma neman yabo saboda siyasa.
Ememobong ya jaddada muhimmancin aiwatar da shirin samar da tsaro a makarantu, wanda ya ce ya ta’allaƙa ne kan bayanan sirri daga al’umma da kuma tsarin ɗaukar matakan gaggawa na dakile hare-hare.
Ya bayyana cewa rashin tsaro ya zama babban cikas ga ilimi a Najeriya, musamman a Arewacin ƙasar. Ya yi nuni da alƙaluman Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da ke nuna cewa Arewacin Najeriya na da mafi yawan yara da ba sa zuwa makaranta—miliyan 10.2 a matakin firamare da miliyan 8.1 a sakandare.
Ememobong ya ce, “Wannan bayanin ba wai kawai yana nuna mummunan hoto ba, har ma yana bayyana ainihin halin da ake ciki a Najeriya. Jerin hare-hare da sace-sace a jihohi daban-daban cikin mako guda na nuna yadda rashin tsaro ya zama sabon yanayin rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin APC ta Bola Tinubu.”
Ya kuma soki yadda gwamnati ke mayar da martani ga sace-sacen ɗalibai, yana mai cewa, “Abin damuwa shi ne, duk lokacin da irin wannan mummunan lamari ya faru, martanin gwamnati ba ya da ƙarfi kuma ba ya nuna tausayi.
“Misali, maimakon Shugaban Ƙasa ya ziyarci jihohin Kebbi da Neja don jajanta wa iyayen da ’ya’yansu ke hannun ’yan bindiga da kuma karfafa jami’an tsaro, sai kawai ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro ya koma Kebbi.”
Ya ƙara da cewa kwatanta yadda aka tura tawagPDP ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.a zuwa Majalisar Dokokin Amurka da taron G-20 da kuma yadda aka tura wakili guda zuwa Kebbi, ya nuna yadda Fadar Shugaban Ƙasa ke ɗaukar wannan matsala da sakaci.”
PDP ta sake jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa shi ne babban aikin kowace gwamnati.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda makarantu Tsaro rufe makarantu da gwamnati
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro.
Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta NejaMai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba.
Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar kowane bayani kafin su yaɗa shi domin kauce wa yaɗs labarun ƙarya.
Wannan bayani ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya na rufe manyan makarantun sakandare 41 da ke yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro, sakamakon sace ɗalibai a jihohin Neja da Kebbi.
Haka kuma wasu jihohi kamar Kwara, Filato, Katsina da Neja sun rufe makarantunsu saboda matsalar tsaro.
Jihar Taraba ma ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu da ke jihar.