2025-11-23@21:19:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8060

«manyan mutane»:

    Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi. Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad. Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan sanda umarnin daina tsaron manyan mutane a faɗin Najeriya. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi. ’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a Bauchi Onanuga, ya ce...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce. Ya ce DPO na Pindiga da shugaban...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai. Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi. An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara...
    Ma’aikatar lafiya a Lebanon ta ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu a wani sabon harin Isra’ila a Kudancin babban birnin Kasar, inda kuma ta raunata kimanin fararen hula 28. A cewar ofishin Firayim Minista Benjamin Netanyahu, harin an kai shi kan “babban hafsan sojojin Hezbollah,” Ali Tabataba’i, wanda Isra’ila ke zarginsa da “jagorantar ƙarfafawa...
    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa an ceto masu ibada 38 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke jihar Kwara. Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya kuma tabbatar da kubutar dalibai 51 cikin 315 da aka sace a jihar Neja....
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar an ceto dukkanin mutanen da mahara suka sace a wata coci a yankin Eruku na Jihar Kwara. ’Yan bindigar sun sace masu ibadar ne a ranar Talata, lokacin da suka kai hari cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Oke Isegun a Eruku, wani gari da ke iyaka...
    Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno. Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan. Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN An rufe duk makarantu a Kebbi Ya ce an sace ’yan natan ne yayin da suke...
    Rundunar Sojin Najeriya, ta ce barin jama’a da aka yi don su kare kansu ne ke rura wutar rikici a Jihar Filato. Birgediya Janar MA Etsy-Ndagi, Shugaban Hulɗar Sojoji Da Fararen Hula ne, ya bayyana haka a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Jos. An rufe duk makarantu a Kebbi Ma’aikatan lantarki na...
     Taron na kasar Brazil akan muhalli wanda shi ne karo na 30 ya amince da bayar da tallafin kudade ga kasashe masu karancin kudaden shiga domin fuskantar matsalar dumamar yanayin duniya.  Mahalarta taron da su ka fito daga kasashen duniya mabanbanta, wadanda suke fafutukar ganin an shawo kan matsalar da ake fuskanta a duniya ta...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya, sakamakon harin da ta ce jami’anta sun fuskanta a Jihar Imo. Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an ’yan sanda ɗauke da makamai ne suka kai wa ma’aikatanta hari a Egbu 132/33kB Transmission...
    161-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi....
    Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita...
    Gwamnatin kasar Venezuela ta gargadi kasar Amurka kan duk wani shirin kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Madoro, a dai-dai lokacin da gwamnatin Trump take bada wani sabon yunkuri nan kusa na ganin ta kwace iko da kasar Venezuela, ta kuma raba Madoro da shugabancin kasar. Kafafen yada labarai da dama sun nakalto manya-manyan Jami’an gwamnatin...
    Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gano wurin da ’yan bindiga suka tsugunar da ɗalibai mata 25 da suka sace daga makarantar kwana ta Maga da ke Jihar Kebbi. A wani taron manema labarai a Birnin Kebbi, Matawalle ya ce a halin yanzu an tsananta aikin leƙen asiri da tsare-tsare,...
    Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa fiye da yara miliyan 400 a faɗin duniya na rayuwa cikin yanayin talauci mai tsanani. A cikin sabon rahoton da ya fitar, UNICEF ya ce ƙarin ɗaruruwan miliyoyin yara na fuskantar hatsarin faɗawa talauci sakamakon katse tallafi, rikice-rikice, da kuma sauyin yanayi da...
    Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA) ta yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalar ambaliyar ruwan da ke addabar al’ummar Ƙaramar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa. Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana hakan bayan karɓar roƙon da jama’ar yankin suka miƙa ta hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar, Jamilu Ɗan Malam Mai...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce matsalar tsaro a yankin Arewa na damunsa matuƙa saboda tana kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya. Ya bayyana haka ne a Jihar Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), wanda Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya wakilce shi. ’Yan sanda sun daƙile harin...
    Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yakin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta nuna damuwarta kan karin hare-haren da ake kai wa mabiya addinin Kirista a Nijeriya. Hegseth ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, yana mai cewa bangarorin biyu sun tattauna...
    Majalisar Dattijai ta nuna damuwa kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar sannan ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta amincewa da daukar akalla matasa 100,000 cikin rundunar sojoji domin karfafa tsarin tsaro na Nijeriya da yake fuskantar kalu bale. ‘Yan majalisar sun kuma yanke shawarar kafa kwamitin musamman domin bincikar yadda...
    Daga Aminu Dalhatu Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara ta ce ta samu nasarar ceto mutune 25 da aka yi  yunkurin sacewa, bayan  wani hari da ’yan bindiga suka kai wa kauyen Kuraje da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau. Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Kuraje da ke gefen birnin Gusau. Wasu gungun ’yan bindiga, ɗauke da makamai ne, suka kutsa cikin ƙauyen suna harbi, lamarin da ya jefa mazauna Kuraje da maƙotan ƙauyukan cikin tashin hankali. Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin...
    Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya fara mayar da rarar kuɗin ga maniyyata, sakamakon rage kudin kujerun Hajjin 2026 da Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya rabawa manema labarai, ya...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ’yan awaren ƙungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu. Obi ya bayyana hukuncin matsayin “abun takaici” kuma alamar gazawar jagoranci. Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin...
    Hukumar Kula da Tsaftace Muhalli da Ababen Hawa ta Jihar Kaduna (KASTELEA) ta ƙaddamar da yaƙin wayar da kan jama’a na watannin ƙarshen shekara na shekarar 2025 a Tashar Motoci ta Malam Nasiru El-Rufa’i da ke ’Yan Ƙarfe, Sabon Gari, Zariya. Taron yaƙin wayar da kan jama’a na  ‘Watannin Ember’ na shekarar 2025 mai taken:...
    Fira Ministan kasar Madagascar Herintsalama Rajaonarivelo ya gabatar da jadawalin ayyukan siyasa a gaban  majalisar kasar, da a ciki ya kunshi yadda zaman gwamnatin rikon kwarya zai kasance da yadda zai kai ga yin manyan zabukan kasar a cikin shekara daya da rabi. Fira ministan kasar ta Madagascar ya kuma ce; A karshen watan farko...
    Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba. A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar...
    Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta...
    160-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi....
    Yawan ɗaliban da aka sace a makarantar Sakandaren St. Mary’s da ke Jihar Neja ya kai 215 da kuma ma’aikata 12 a cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN). Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Neja, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya ce mutum 227 aka sace a makarantar, ɗalibai 215 da kuma malamai 15....
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Iran mohammad Bhakir Qalibaf ya bayyana cewa makiya JMI sun sawya salon yakaar kasar kamar yadda suka saba, a halin yanzu sun fibada karfi kan takurawa tattalin arziki da rikita al-adu da kuma zamantakewa tsakaninmutanen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP  nakasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya jumm’a...
    Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr...
    A ranar Alhamis da ta gabata ce karamin kwamiti mai kula da al-amuran nahiyar afirka a majalisar dokokin kasar Amurka ya bude tattaunawa dangane da zargin da shugaban kasar Donal Trump yake yin a cewa ana kashe kiristoci a tarayyar Najeriya fiye da duk wata kasa a duniya. Wanda hakan ya say a yi barazanar...
    Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci saboda yawaitar sace-sacen ɗalibai da malamai a Najeriya. Atiku, ya yi wannan kira ne bayan harin da “yan bindiga suka kai yankin Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a...
    Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe...
    Jami’an rundunar ’yan sanda ta Jihar Delta sun kama wani fasto na cocin Omega da ke Sapele bisa zargin lalata, fyade da kuma cin zarafin mata uku. Ana zargin Faston, wanda aka bayyana sunansa da Daniel Ololo mazaunin garin Sapele da yin lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne. Gwamnatin...
    ’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama. A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya.   Yayin da gwamnati ke cewa hukuncin ya biyo bayan dogon shari’a da...
    Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran...
    Ƙaramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin “wadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,” sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan...
    Ƴan ta’adda sun kai hari Makarantar St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara da ke Jihar Neja a Najeriya, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makaranta da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu. Rahotanni daga makarantar sun ce harin ya faru ne da tsakar dare, kuma tuni aka fara...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u ‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka...
    Daga Usman Muhammad Zaria Daliban makarantu daga jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, Jigawa da Katsina sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su samar musu da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, da taftataccen ruwan sha. Daliban sun yi wannan kiran ne yayin bikin Ranar Yara ta Duniya da aka gudanar...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana...
    Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga,...